An Gudanar Da Walimar Haddar Alƙur’ani Ga Ɗalibai 21 A Tarteelil Ƙur’an Wattajweed.

Daga Ibrahim Muhammad

Madarasatul Tarteelil Kur’an Wattajweed da ke kusa da Almuntada kusa da masallacin marigayi Shaikh Ja’afar Adam da ke Ɗorayi Kano, ta gudanar da walimar haddar Alƙur’ani mai girma na ɗalibai 21 karo na biyar a ɗakin taro na sabuwar Jami’ar Bayero ranar Lahadi.

A jawabinsa a wajen taron, shugaban Tsangayar Ƙur’ani na Jami’ar Bayero, Farfesa Ahmad Murtala, wanda Dakta Ibrahim Ahmad Indabawa ya wakilta ya ce, idan aka yi duba da ƙanƙantar shakarun ɗaliban da suka yi haddar al’umma na da ƙarfin gwawar gaba za ta yi kyau a tsakanin matasa masu tasowa.

Ya yi kira ga mahaddatan kan su yi ƙoƙarin ɗabbaka Ƙur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum.

Sannan ya taya iyayen yaran murna da suka sa su a makarantar Ƙur’ani da hadda a wannan yanayi da mutane suka fi karkata da son abin duniya.

Dakta Ibrahim Ahmad Indabawa ya ja hankalin iyayen ɗaliban su riƙa ba da kulawa ga malamai da makarantar su riƙa kai ziyara lokaci zuwa lokaci.

Ya nuna damuwa a kan yadda mafi yawan iyaye ba sa kai ziiyara a irin waɗannan makarantu da hakan bai kamata ba, domin ziyarar za ta ƙara wa malaman makarantar ƙwarin gwiwa.

A saƙon shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa ya taya waɗanda Allah ya azurta da haddar Ƙur’ani murna da yi wa iyayensu fatan alheri ba da kulawa da karatun yaran.

Ya kuma yaba wa malamam makarantar da suka tsayu wajen karantar da ‘ya’yan Musulmi haddar Ƙur’ani.

Daraktan makarantar Malam Abubakar Aminu Tafida da ya fi shahara da Malam Siddik ya ce, taron na walimar taya murna ne ga ɗalibai 21 da suka yi hadda, wanda kuma taron shi ne karo na biyar tun kafa makarantar.

Ya ƙara da cewa an kafa makarantar ne a 2011, wacce ta faro da ɗalibai da basu kai 20 da malamai biyu, amma yanzu cikin ikon Allah suna da ɗalibai sama da 300 da malamai 23, suna kuma da kyakkyawan dangantaka da iyayen yara, suna ba su gudunmuwa na abin da makaranta ke buƙata na zuwan yara da kiyaye dokoki da biyan kuɗin makaranta.

Daraktan makarantar ta Tarteelil Ƙur’an Wattajweed ya ƙara da cewa, suna ba da muhimmanci ga tarbiyya da ba da ingantaccen ilimi, ba a sakaci da su a tafiyar makarantar.

Sai dai ya nuna damuwa da yadda wasu iyaye ke janye ‘ya’yansu saboda wani buri na ilimin duniya da ake so su goge ko yanayin rayuwa, bayan makarantar ta ɗora su a kan tsari da za su yi hadda.

Malam Abubakar Aminu Tafida ya ja hankalin iyaye da cewa idan suka tsaya wa ‘ya’yansu suka haddace Ƙur’ani Allah zai hidimta musu da alkhairi mai yawa.

Ya kuma nuna matuƙar farin cikinsa bisa karramawa da iyayen ɗaliban sukayi masa a yayin gudanar da walimar.

A yayin taron walimar dai an raba kyautuka ga ɗalibai da suka fi nuna hazaƙa a yayin musabaƙar da naɗa gwarazan shekara na Ƙur’ani na makarantar ɗaya a ɓangaren mata ɗaya daga ɓangaren maza.

Makarantar ta gabatar da bayar da tallafin yin karatu ga wasu ɗalibanta da wasu daga malamai.

  • Related Posts

    WOTCOSA Ajin 1975 A Shekara 50: Sun Karrama Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje Da Tagwayen Lambobin Yabo

    Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban tsohuwar makarantar horon malamai ta mata ta Kano (WTC), Women Teachers College Old Girls Association (WOTCOSA) da yanzu ake kiran a makarantar da Goverment Girls College (WTC)…

    Ɗaliban Ƙaramar Hukumar Dala Da Gwamnatin Kano Za Ta Tura Manyan Jami’o’i Na Cikin Gida Da Ƙasashen Waje Karatun Digiri Na Biyu, Sun Yi Taron Nuna Godiya

    Daga Ibrahim Muhammad Ɗalibai ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala da za su tafi karatu manyan jami’o’i a ciki da wajen ƙasar nan da gwamnatiin jihar Kano ta ɗauki nauyinsu sun…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?