Daga Ibrahim Muhammad
Al’ummar Musulmi a Nijeriya sun buƙaci mahukunta su saki jagoran al’ummar Palasɗinawa mazauna ƙasar nan, Ransy Abu Ibrahim da aka kama aka tsare ba tare da ya aikata wani laifi ba.
Da yake magana da ‘yan jarida a jihar Kwara ɗaya daga cikin al’ummar Musulmi shugaban ƙungiyar Harakatul Islamiyya, Malam AbdulRazaƙ Abdulwahab Al-Ameen ya ce jagoran Palasɗinawan Ransy Ibrahim yana zaune a ƙasar nan sama da shekaru 30 ba a taɓa samun sa da wani abu na karya doka ba.
Ƙungiyoyin suna zargi Isra’ila da hannu a sa wa hukumomin ƙasar nan su kama jagoran Palasɗinawan da har yanzu hukumomi ba su bayar da wani bayani kan dalilin kama shin ba.
Ya ce Palasɗinawa a ƙasar nan shekara da shekaru na zaune lafiya da al’umma, don haka take haƙƙinsu ne, kama jagoransu da bai aikata wani laifi ba.
Ƙungiyoyin addinin Musulunci sun ja hankalin gwamnatin ƙasar nan cewa ta saki shugaban Palasɗiwan domin ƙar ci gaba da riƙe shi ya harzuƙa al’ummar Musulmi da sauran mutane masu son ganin an yi adalci su soma fitowa suna nuna wa gwamnati rashin yarda.
Sannan ya shawarci gwamnatin ta guji yin alaƙa da Isra’ila da kullum aikinsu zubar da jinin al’umma ne.






