Mon. Nov 3rd, 2025

Assasa Farfaɗo Da Al’adun Gargajiya; Gwamnatin Kano Ta Yi Abu Mai Kyau -Hon. Tukur Muhammad Wada

By Saleh Aliyu Oct 26, 2025

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana assasa farfaɗo da al’adunmu na gargajiya da ware ranaku na musamman a jihar Kano a matsayin wani muhimmin abu, kuma abin alfahari ne da farin ciki da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon. Tukur Muhammad Wada ne ya bayyana hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai a rumfar da suka baje koli a wajen taron farfaɗo da al’adu da aka yi a Kano.

Ya ƙara da cewa kamar masarautarsu ta Rano suna da kyakkyawan tarihi na sarauta da zamantakewa da sana’o’i da suka yi fice a kai, “Don haka muna murna da wannan taro na farfaɗo da al’adu,” in ji shi.

Ya ce su ma a matakin ƙaramar hukumar Rano za su cigaba da assasa al’adun gargajiya ta hanyar fito da abubuwa da ba a sani ba na al’adun al’umma, domin na baya su sani su riƙe su yi alfahari da su.

Hon. Tukur Muhammad Wada ya yi kira ga al’ummar Rano da ma jihar Kano baki ɗaya a kan su san cewa riƙo da kyawawan bal’adu da suka gada yana da muhimmanci, kuma zai ƙara musu kima a idon duniya muddin suka riƙe su da kyau.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *