Daga Ibrahim Muhammad
An yi kira ga ma’aurata musamman su zama masu girmama juna da sanin ya kamata da yin haƙuri a tsakaninsu.
Ɗan Malisar jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Gezawa, Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara ne ya yi kiran a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ɗaura auren ‘yarsa Ubaidah Abdullahi Yahaya da Angonta Zayyanu da aka yi a babban masallacin Juma’a na garin Tsamiyar Kara bayan idar da Sallah.
Ya yi nuni da cewa shi aure muhimmin ibada ne, kuma Sunnah ce ta koyi ga Manzon Allah ga al’ummar Musulmi, kuma mutuntaka ce ga dukkan ɗan’adam, don haka abu ne mai muhimmanci ma’aurata su zama masu darajanta juna da girmamawa a tsakanin su.
Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara ya jaddada cewa ta hanyar aure ne ake samum kyakkyawar zuriya da ake fatan ta zama ta gari da za su tashi da kyakyawar tarbiyya da iyaye za su raine su a kai, dan haka ma’aurata su yi ƙoƙarin gina kyakkyawar zamantakewa a tsakaninsu da zai naso a kan zuriyarsu.
Ɗan majalisar dokokin na jihar Kano mai wakitar Ƙaramar hukumar Gezawa, Hon. Yahaya ya gode wa ɗimbin al’umma da suka haɗa Hakimi da shugaban jam’iyyar APC na Gazawa da ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da jami’an tsaro da iyayen ƙasa da sauran al’umma bisa halartar ɗaurin auren.






