Daga Ibrahim Muhammad Kano
Mai taimaka wa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunubu a kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya ce takarar shugabancin ƙasar nan da ake cewa tsohon shugaban ƙasa Goodlock Jonathan zai yi, ba wani abin tsoro ba ne a wajensu, ko kuma wani abu da zai tayar musu da hankali.
Ya yi nuni da cewa batun takarar na Goodlock ba jita-jita ba ce, domin na hannun damar tsohon shugaban ƙasar Farfesa Jerry Gana, wanda jigo ne a tafiyar, ya fito ya ayyana cewa Goodlock Jonathan zai yi takara.
Abdulaziz Abdulaziz ya ce, su takarar tsohon shugaban ƙasar ba abin tsoro ba ce, ba kuma wani abu ne da zai tayar da hankali ba ko ya sa su fargaba ba, shi ya sa ma suka fito su ka yi maganar cewa suna maraba da shigowarsa takarar in har ya yanke hukuncin yin takarar za a haɗu a filin dagar zaɓe, a ƙarshe duk wanda jama’a suka yarda da shi shi ne zai samu.
Abdulaziz ya ce ba su ɗauki maganar takarar Jonathon jita-jita ba, domin su babu yadda za a yi su fiio su mayar wa jita-jita martani. Saboda haka suna cikin shirin ko ta-kwana, babu gudu, babu ja da baya, duk masi son su yi takara su fito ga fili ga mai doki tsakanin su da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu a 2027.







