Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana cewa Dakta
Muhammad Musa Zango da cewa mutum ne mai mutuntaka da tasiri da tasa mutane ke alfahari da shi a cikin dukkan wani abu da ya haɗa su.
Alhaji Bala Alpha ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin bukin karramamawa da aka yi wa Dakta Muhammad.
Ya ce a matsayinsu da suke tare da shi tun da ya san shi bai taɓa ganin sa a cikin fushi ba ko me za ku yi da murmushi yake. “Mutum ne shi haziƙi, duk abin da ya sa a gaba ba ya gazawa a kai,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “A ma’amalarmu da shi shekara da shekaru, kullum cikin fara’a yake. Duk lokacin da wani abu ya taso na alheri za ka ga ya sadaukar da kansa a kai domin cimma nasara. Don haka wannnan karramawar ta cancance shi,” ya jaddada.
Alhaji Bala Alpha ya yi kira ga al’ummar Zango yadda suka kalli kyawawan halaye da gudunmuwa da yake bayarwa suka karrama shi suka ƙulla wannan danƙon zumunci su ci gaba da fata. “Allah ya yi musu jagoranci a kai domin al’umma da suke tasowa da na gaba su san cewa sadaukar da kai ga al’umma da yankinsu yana da mutukar muhimmanci da tasiri wajen haɗin kai.






