Ba Za Mu Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba -Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sake jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta taɓa shiga sulhu da ‘yan bindigar da ke haddasa ta’addanci a Jihar Zamfara ba.

A ranar Larabar nan ne gwamnan ya halarci wani gangami da matasan Zamfara suka shirya mai taken ‘Tafiyar Zaman Lafiya’.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, wata gamayyar matasan Zamfara sun shirya tattaki domin samar da zaman lafiya da haɗin kai, domin murnar zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya. 

Ya ƙara da cewa, an fara wannan gangami ne daga gidan gwamnatin jijar, wanda kuma aka ƙare a dandalin Freedom, inda dubban mutane suka taru domin nuna goyon bayansu ga gwamnati a yaƙin da take yi da ’yan bindiga.

Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa a shirye yake ya yi duk wata yiwuwa domin ganin an dawo da zaman lafiya a dukkan sassan Jihar Zamfara.

“Ina so in gode wa ƙungiyar haɗin gwiwar matasa da suka shirya irin wannan muhimmin ‘tattakin zaman lafiya’ saboda muna buƙatar irin wannan shiri a wannan mawuyacin lokaci.

“Muna da dogon tarihi na kasancewa mutane da jiha masu zaman lafiya. Duk da haka, a cikin ‘yan shekaru, abubuwa sun canja sosai. Wannan yana buƙatar nazari don ganin inda muka yi kuskure da yin gyare-gyaren da suka dace. Tsaro alhakin kowa ne; dole ne mu bada haɗin kai da goyon bayan tsarin.

“A koyaushe ina maimaita cewa; babu wani abu wai shi “sulhu” da ‘yan ta’adda, mun ga yadda gwamnatocin baya suka yi yunƙurin sasantawa, wanda hakan ya ƙara wa ’yan bindiga ƙwarin gwiwa.

“A wannan ranar dimokuraɗiyya, kuma da bukukuwan Sallah, ina mai farin cikin sanar da cewa na amince da biyan albashin watan Yuni ga ma’aikatan jihar Zamfara, baya ga albashin, mun cika alƙawarin da muka ɗauka na aiwatar da mafi ƙarancin albashin Naira dubu 30, saɓanin yadda aka saba da dubu bakwai.

“Zan ci gaba da aiki don ci gaban jihar mu da kuma tallafa wa mutanen mu. Mun samu ci gaba sosai a fannin tsaro, ilimi, noma, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafawa da dai sauransu.

“Da wannan zaman lafiya, mun aike da saƙo mai ƙarfi ga maƙiya jihar cewa mun haɗa kai a matsayin mu na al’umma, kuma gwamnati ta jajirce wajen ganin ta kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga a Jihar Zamfara.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano