Babu Mai Gidan Biredin Da Yake Amfani Da Sinadarin Da Zai Cutar Da Al’umma -Alhaji Ɗahiru Ɗantsoho

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana ranar ingancin kaya ta duniya da cewa rana ce ta farin ciki ga duk wani da yake sana’a ta kamfani ko yake sarrafa kayan masarufi, saboda rana ce da take nuna ‘yancin kayayyaki na duniya gaba ɗaya tun daga kan abinci, sutura da abin hawa da kayan gini da sauran abubuwa masu amfani ga rayuwar dan’adam.

Alhaji Ɗahiru Muhammad Ɗantsoho shugaban ƙungiyar masu gidajen birodi na jihar Jigawa, kuma Daraktan gudanarwa na kamfanin biredin Lautai, wanda kuma shi ne Manajan Daraktan na ZSB Bakery And Global Resources ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ce Hukumar kula da ingancin kayayyaki (SON) na ba da gudunmawa matuƙa wajen inganta kayayyaki da ake mu’amala da su a tsakanin al’umma kuma suna aiki tare da ita a kowane lokaci domin tabbatar da ingancin sana’arsu.

Da yake tsokaci a kan ƙorafin da ake na rashin samun sauƙi a farashin burodi a jihohin Kano da Jigawa a wannan lokaci da ake cewa an sami rangwame a fulawa, ya tabbatar da cewa, an samu ɗan sauƙi a fulawa, amma ba fulawa ce kaɗai ake sarrafawa ta zama burodi ba, ana amfani da abubuwa kusan guda 20 da ake sa wa kafin burodi ya amsa sunansa a kai ga sayarwa.

Ya ce daga cikin kayayyakin fulawa ita kaɗai ce ta ɗan rage kuɗi da bai wuce 3000 ba, kuma a duk buhu na fulawa a kan iya yin biredin da in an ce za a rarraba 3000 a cikin buhu ɗaya na fulawa ba lallai wani biredin ma ya san an rage masa girma ko an ƙara masa ba. “Saboda haka ragin da aka samu ba shi da ƙarfin sa biredin ya rage kuɗi, ko kuma masu ci su gane cewa an ƙara masa girman da zai tabbatar da kaya sun rage kuɗi,” in ji shi.

Ya ƙara da nuni akwai fetur, gas, sukari, gishiri, leda, yis da sauran abubuwa da dama suna cikin abin da ake sa wa, duk babu abin da ya rage da zai sa shi mai cin biredin ya gane wannan abin bai shafi tsari na biredin ba, saboda su ma in an samu ƙari a kasuwa ba sa rage girmansa.

Ɗahiru Muhammad Ɗantsoho shugaban ƙungiyar masu Biredi na jihar Jigawa ya ce a halin yanzu suna sa ran sun gama yaƙar abubuwa da ake sa wa a biredi masu cutarwa ga lafiyar al’umma, saboda ko su a matakin ƙungiya sun shiga lungu da saƙo sun gayyaci ƙwararru na harkar lafiya da ingancin abinci sun kira su sun wayar da kan masu gidajen biredi sun nuna musu cewar wasu abubuwa ma idan ka sa su a sana’arka, sai dai ma a maimakon riba sai ma ka sami faɗuwa, saboda suna rage yawan riba da za a samu yanzu duk babu wannan a harkar yin biredi.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?