Daga Ibrahim Muhammad
Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta labarin da ake yaɗawa na cewa ya rubuta wa jam’iyyar APC buƙatar shiga cikin ta.
A rana Slhamis ne aka yi ta yaɗa labarin har aka ce hakan ne dalilin da ya sa masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC na jihar Kano suka gudanar da wani taron gaggawa a Abuja.
A cikin wata sanarwa da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya fitar da safiyar ranar Juma’a ya ce labarin ba shi da tushe balle makama.
“An wayi gari da yaɗa jita-jita a kafafen sada zumunta cewa mun gabatar da takardar nuna sha’awar shiga wata jam’iyyar siyasa a ƙasar nan”, n ji Kwankwaso.
Ya fito fili ya nesanta kansa daga wannan batu, da ya bayyana cewa, “ba mu taɓa miƙa irin wannan takarda ga kowacce jam’iyya ba'”.
Sanarwar Jagoran Kwankwasiyya jigon jam’iyyar NNPP na ƙasa ya ce yana shawartar jama’a da su ci gaba da bibiyar sahihan hanyoyin da aka tanada ta ofishinsa domin samun ingantattun bayanai game da abubuwa da ya sa a gaba.







