Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnatin Tarayya ta nuna mutuƙar jin daɗin ta ga Madugun Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tare da gode masa bisa kishin ƙasa da ya nuna na mayar da martani ga maganganu da shugaban Amurka ya yi Trump na barazanar yiwuwar kawowa Nijeriya hari
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana matsayar Kwankwaso abu ne da ya dace dukkan shugabannin siyasa su yi ba tare da la’akari da jam’iyya ba, su haɗa kai su tsaya waje ɗaya don kare ƙasarmu a matsayin ‘yan ƙasa na gari.
Ya bayyana matsayar Kwankwaso a matsayin ta kishin ƙasa, yana kira ga sauran shugabannin jam’iyyun adawa su bar siyasa a gefe, su tsaya tsayin daka wajen kare martabar ƙasar nan a gaban abin da ya kira “ɗaukacin ƙalubalen waje.”
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a shafiinsa na X ya yi Allah wadai da matsayar Trump na kiran ƙasar nan mai damuwa ta musamman bisa zargi mara tushen na cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla.
Tsohon Gwamnan na jihar Kano, wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya yi gargadin cewa maganar Donald Trump na iya tayar da hatsaniyar addini da ta’azzarar matsalar tsaro a ƙasar nan, kuma ya yi jan hankali ga shugaban na Amurka maimakon wannan kamata ya yi ya tallafa wa ƙasar wajen kawar da matsalar barazanar tsaro.








