Fasahar Zamani Za Ta Taimaka Wajen Shawo Kan Matsalar Tsaro A Ƙasar Nan -Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar amfani da manyan na’urorin zamani domin yaƙi da matsalar tsaro a Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.

Gwamnan Jihar Zamfara da wasu gwamnonin jihohi sun gana da Amina J. Mohammed, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Washington D.C. ranar Juma’a.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Zamfara, Benuwai, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, da Neja.

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed ta yaba wa Gwamnonin kan ƙoƙarin da suke yi na ganin an magance matsalolin yankin.

“Kasancewar ku a nan ya nuna ƙwaƙƙwarar sha’awar da Gwamnonin Arewa ke yi na aiwatar da sauyi a jihohinsu.

Da yake bayyana halin da ake ciki a Zamfara ga Mataimakin Babban Sakataren, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana muhimmiyar rawar da fasahar zamanj za ta iya takawa wajen inganta tsaro da kuma buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen amfani da ƙarfin fasahar da ta haɗa da yin amfani da fasahar ƙere-ƙere, na’urorin tantance kwayoyin halitta da kyamarorin sa ido (CCTV).

“Muna nan da matsalolin da dama, amma babban ƙalubalen mu shi ne rashin tsaro, kuma dole ne a yi wani abu a kai.

“Saboda rashin tsaro, noma ya gagara. Muna buƙatar taimako wajen bunƙasa noma ta yadda za mu iya tura fasahar yaƙi da wannan tada ƙayar baya. Muna fatan samun mafita ga waɗannan matsalolin yayin waɗannan tarukan. Na karɓi mulki a jiha mai cike da rashin aiki tare da ƙarancin ci gaba.

“Na ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi da lafiya. Dole ne mu ɗauki matakin gaggawa don magance waɗannan batutuwa masu muhimmanci; in ba haka ba, makomar mu za ta yi muni. Muna buƙatar tallafi mai muhimmanci don shawo kan waɗannan ƙalubalen da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga jama’armu.”

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano