Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana cewa bikin da aka gudanar na cika shekaru100 da fara saukar jirgin sama a jihar Kano da cewa abin farin ciki ne da jin daɗi ga tarihin fara saukar jirgin sama a ƙasar nan.
Hon. Dakta Aliyu Ibrahim, wanda National Convener National Agenda for Tinubu 2027-NAFT.27, wanda ya wakilci shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan ga ‘yan jarida a yayin taron shekara 100 da soma saukar jirgin sama a Kano da makarantar Caliphate Aviation Training da haɗin gwiwar Hukumar FAAN suka gudanar a Kano.
Ya ce sun ji daɗin yadda wannan makaranta ta bayar da horo a kan harkokin aikin jirgin sama ta Caliphate Aviation da haɗin gwiwar hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa suka shirya wannan muhimmin taro na tarihi, hakan wani mataki ne na sawa a tuna abubuwa da aka yi a baya da abin da ya kamata a yi domin haɓaka cigaban harkokin filayen jiragen da sufurinsa musamman ma a jihar Kano.
Ya ce a matsayinsa na wakilin shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama na kasa FAAN, tsohon Gwamnan jihar Kano, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje suna da tabbacin shugaban FAAN na ƙasa zai yi aiki tuƙuru don bunƙasa cigaban filayen jiragen sama daidai da zamani.
Ya ƙara da cewa a harkar jirgin sama a ƙasar nan akwai buƙatar a ƙara ƙoƙari da zage damtse kuma ya san Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai kawo gyara a filin jirgin sama na Kano da sauran filayen da suke faɗin ƙasar nan.
Dakta Aliyu Ibrahim ya ce lambar yabo da ya karɓa a madadin shugaban Hukumar FAAN, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya wakilta a wannan taro mai cike da tarihi na cikar Kano shekara 100 da soma saukar jirgin sama, zai ƙara masa ƙwarin gwiwa na aiwatar da aiki tuƙuru a Hukumar.






