Daga Ibrahim Muhammad
Kamar yanldda aka saba, sama da marayu 2000 ne a garin Haɗejia za su amfana da kayan abinci da na Sallah da Gidauniyar Abdullahi Rara ta za ta raba.
Shugaban Gidauniyar, Alhaji Abdullahi Rara ne ya bayyana hakan a wajen tantance waɗanda za su amfana da tallafin.
Ya ce kamar yadda suka saba taimaka wa marayu da yi musu ɗinki da sauran hidindimu da suke yi, bana ma sun soma shirye-shirye a kai.
Ya ce, “Wannan karon ma Allah ya kawo mu. Dama mukan soma shirye-shirye ne daf da shigowar watan Azumin Ramadan, mu kira teloli maza da mata sama da 30 mu ba su ɗinkunan yara marayu su yi,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa zai kai har cikin Azumi ana ɗinka kayan a ƙarshen kwanakin Azumi ranar 27 suke fara rabon kayan ga har zuwa ragowar kwanakin Azumi har bayan Sallah.
Alhaji Abdulahi Rara ya yi kira ga masu hali a cikin al’umma a kan su riƙa tallafa wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi a cikin al’umma domin rabauta a duniya da lahira.






