Sat. May 10th, 2025

Gwamna Lawal Ya Karbi Baƙuncin Jami’an Hukumar NSCDC 10 ‘Yan Asalin Zamfara Da Suka Samu Ƙarin Girma

By Gazali Haruna Apr 27, 2025

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya karbi baƙuncin jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) su goma ‘yan asalin jihar bayan samun ƙarin girma.

Jami’an da aka yi wa ƙarin girma sun samu jagorancin kwamandan NSCDC na shiyya 2, ACG Haruna Bala Zurmi, a wata ziyarar ban girma da suka kaiwa gwamnan a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce manyan jami’an hukumar NSCDC da aka yi wa ƙarin girma abin alfahari ne ga al’ummar Zamfara kuma alama ce da ke nuna cewa ana samun ci gaba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an ƙara wa jami’an girma tare da yi musu ado zuwa ga manyan muƙamai a cikin rundunar; uku (3) sun samu ƙarin girma zuwa muƙamin Mataimakin Kwamandan Janar (ACG), yayin da sauran bakwai suka samu ƙarin girma zuwa muƙamin Kwamandan Rundunar (CC).

A yayin jawabinsa, Gwamna Dauda Lawal ya ƙarfafa gwiwar jami’an da su ci gaba da sanya Zamfara a zukatan su yayin da suke yi wa ƙasa hidima.

Ya ce, “Dukkanmu mun damu da Zamfara saboda ba mu da wani waje da muke kira gida, idan ka yi ritaya daga aiki za ka dawo nan, don haka aikinmu na haɗin gwiwa shi ne mu ɗaukaka jiharmu.

“Kwamandan babban aminin jihar Zamfara ne, ina so in yi amfani da wannan dama domin na gode masa bisa ga ɗimbin taimakon da ya yi mana a yaƙin da muke yi da rashin tsaro.

“Lokacin da na ji labarin ƙarin girma da ku ka samu, na yi marmarin haɗuwa da ku, aƙalla don shirya liyafar cin abinci don girmama ku, wanda ba shakka za mu yi, mafi muhimmanci, na yi farin ciki da nasarar da ku ka samu – wadda ta ksance ta al’ummar Zamfara ce.

“Kamar yadda na ambata, muna da haƙƙi na haɗin gwiwa don bunƙasa Zamfara, za mu ci gaba da buɗe hanyoyin sadarwa ta yadda duk wani ƙalubalen da muka fuskanta za a sanar da ku, tare da ba da damar bayar da shawarwari masu muhimmanci, ƙofata a buɗe take ga shawarwari, da kuma tattauna batuttuwa masu ma’ana. Dukkanmu za mu yi farin ciki idan Zamfara ta inganta. Na gode da ziyarar tare da taya ku murna.”

Tun da farko, shugaban tawagar kuma kwamandan NSCDC na shiyya ta 2, ACG Haruna Bala Zurmi, ya bayyana cewa irin gudunmawar da Gwamna Lawal ya bayar ne ya sa aka ƙara musu girma, inda ya ce ba a taba samun ƙarin girma har na jami’ai 10 a lokacin guda a tarihin Sibil Difens a jihar ba sai a wannan lokaci.

“Abin da muka yi imani da shi ne cewa wannan karimcin na Kwamandan Janar bai rasa nasaba da goyon baya da taimakon da jami’an tsaro da jami’an NSCDC ke samu a jihar Zamfara a ƙarƙashin gwamnatinka da kuma kyakkyawar kulawarka. Muna nan ne albarkacin ka.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *