Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu Na Tafkar ‘Yan Nijeriya Da Ɗayen Kara -Mustapha Muhammad Tinubu

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu da cewa mutum ne mai son cigaban al’umma, amma sai dai ba shi da mashawarta a gwamnatinsa masu kishi da a ce akwai irin su Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso jagorancin Kwankwasiyya a kusa da shi da talaka ya yi sambarka.

Hon. Mustapha Muhammad Tinubu (Chiranchi) jigo a tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai bayan ɗaurin aure da aka yi na ‘ya’yansa.

Mustapha Tinubu, wanda ya bayyana cewa sunansa da ake lakanawa da Tinubu a ciki ya samo asali ne saboda zama da suka yi da shugaban ƙasa na yanzu Bola Ahmad Tunibu a shekarar 1999 a Agege a jihar Legas yana ɗaya daga cikin yaransa, wannan shi ne abin da ya kawo ake kiransa da sunan sai kuma ya yi tasiri.

Sai dai Hon. Mustapha Muhammad Tinubu ya ce sai dai ga shi ƙarƙashin gwamnatin Ahmad Bola Tinubu ma tarayyar ƙasar nan ana ta tafkar ‘yan Nijeriya da ɗayen kara. Wannan abin kaico ne sai suna fata Allah ya saisaita shi ya shigo da irin su jagoransu Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso su sai ta ƙwaƙwalensa su sai ta tafiyarsa a kori waɗanda suke ƙyama da kin talaka.

Da yake magana a kan masu cewa yana hidima ga tsarin Kwankwasiyya tun a baya har yanzu suna da gwamnati, amma ba wani abu na muƙami da aka ba shi, ya ce komai da aka gani yin Allah ne, kuma Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf yana sane da su, kuma komai lokaci ne duk abin da ka ga ya same ka daga Allah ne lokacin da ne ya zo, ba makawa sai an yi shi suna godiya ga Jagoran kwankwasiyya da Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin kulawa da ake ba su.

Alhaji Mustapha Muhammad Tinubu ya kuma musanta cewa akwai ‘yan adawa da suke zaɓarinsa ya koma cikin su. Ya ce duk wanda ya ce ma zai zabarin sa zai wahaltar da kansa ne, sai dai idan ma ta kama ma jagoransu na Kwankwasiyya ya shiga APC ɗin, za su bi shi saboda zai gyara mata yanayi ne, ta zama mai tsafta da talakawa za su amfane ta. Don haka shi babu ma wani mutum ma da zai ga idon ma da zai zabare shi a matsayinsa na ɗan Kwankwasiyya.

Alhaji Mustapha Muhammad Tinubu ya yi godiya ga Allah da Gwamnan jihar Kano bisa turo wakilai da ya yi zuwa ɗaurin auren da aka yi, kuma ba abin da zai ce al’umma sun amsa kira Allah ya saka da alkhairi.

Mustapha Muhammad Tinubu ya ce kullum suna zaune da jama’a lafiya, kuma suna godiya ga Allah da ya haɗa kansu a tsarin tafiyar Kwankwasiyya suna tare tsintsiya maɗaurinsu ɗaya ƙarƙashin Jagora Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.

Alhaji Mustapha Muhammad Tinubu ya gode wa hadiman Gwamna irin Kwamishinoni da masu bai wa Gwamna shawara da shugabannin ƙananan hukumomi waɗanda suka sami zuwa ta ya shi murna da waɗanda suka yi wa aike Allah ya saka musu da alheri.

  • Related Posts

    WOTCOSA Ajin 1975 A Shekara 50: Sun Karrama Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje Da Tagwayen Lambobin Yabo

    Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban tsohuwar makarantar horon malamai ta mata ta Kano (WTC), Women Teachers College Old Girls Association (WOTCOSA) da yanzu ake kiran a makarantar da Goverment Girls College (WTC)…

    Ɗaliban Ƙaramar Hukumar Dala Da Gwamnatin Kano Za Ta Tura Manyan Jami’o’i Na Cikin Gida Da Ƙasashen Waje Karatun Digiri Na Biyu, Sun Yi Taron Nuna Godiya

    Daga Ibrahim Muhammad Ɗalibai ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala da za su tafi karatu manyan jami’o’i a ciki da wajen ƙasar nan da gwamnatiin jihar Kano ta ɗauki nauyinsu sun…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?