Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa matasa ta hanyar samar da ayyukan yi masu ɗorewa, faɗaɗa damar koyon sana’o’i, da ƙarfafa yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi.
Wannnan na ƙunshe ne cikin sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar domin tunawa da Ranar Matasa ta Duniya na wannan shekarar ranar Laraba.
Ya bayyana cewa matasa sune ginshiƙin canjin tattalin arziƙi da zamantakewa don haka suka sake buɗe cibiyoyin koyon sana’o’i daban-daban da hakan ya ba dama ga dubban dogaro da kai.
Ba ya ga samar da ayyuka ga matasa a sassa da dama da suka haɗa da na kiwon lafiya da ɓangaren ilimi da na gona da sauran sassan ayyukan gwamnati da yawa.
Gwamnatin jihar Kano ta ce tana shirin sake buɗe Cibiyar Gyara Hali na Ƙiru don gyara tarbiyyar matasa musamman masu amfani da miyagun ƙwayoyi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce nasarorin da aka samu bayan haɗa ta kafuwar Hukumar KASITDA da kuma nasarar shirya taron ƙasa da ƙasa kan Fasaha da na’ura mai ƙwaƙwalwa.
Ya ce hakan na daga wasu muhimman matakai na sanya Kano a tsari na zama cibiyar ƙirƙira da ƙwarewa a kan sanarwar zamani.
Gwamnan na jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Yusuf ya yi kira ga shugabannin al’umma, iyaye da malamai, da ƙungiyoyi masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma su haɗa kai wajen samar da yanayi na aminci da haɗin kai domin kyautata cigaban matasan jihar Kano su zama masu amfani.






