Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnatin jihar Kano ta ƙuduri aniyar kashe ɓeraye a ƙaramar hukumar Garun Malam don daƙile barazanar yaɗuwar cutar Lassa.
Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Nabulus Abubakar Ƙofar Na’isa.
Sanarwar ta ce ya zama wajibi gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa domin a kare lafiyar al’umma sakamakon tabbatar da an daƙile ɓullar cutar ta Lassa a ƙaramar hukumar Garun Malam da ta yi sanadin rasuwar wata mata.
Dakta Abubakar Labaran ya ce an killace duk masu mu’amala da wacce ta rasun da suka haɗa da mijinta da kuma jami’an lafiyar da suka ba ta kulawa lokacin da aka kawo ta asibiti.
Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mijin matar da ta rasu a sanadiyar cutar da ɗaya daga cikin ‘ya’yanta sun kamu da cutar ta Lassa.
Dakta.Abubakar Labaran Yusuf ya yi nuni da ɗaukar matakin kashe ɓerayen a yankin a wani mataki na daƙile yaɗuwar cutar kasancewar ɓeraye na ɗaya daga manyan hanyoyin yaɗa cutar ta Lassa.
Ma’aikatar Lafiyar ta jihar Kano ta ja hankalin mafarauta su guji farautar ɓeraye, su kuma riƙa ɗaukar matakan kariya domin hana yaɗuwar cutar daga jikinsu zuwa ga sauran mutane.
Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya shawarci jama’a da su yi hanzarin sanar da jami’an lafiya mafi kusa da su idan suna zargin cutar Lassa.
Sannan ya buƙaci jami’an lafiya su ɗauki matakan kariya yayin da suke kula da waɗanda aka samu da cutar domin samun kariya da kaucewa yaɗa ta ga sauran jama’a.






