Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Wutar Lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana A Asibitin Malam Aminu Kano

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin megawatt bakwai a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) bayan rikicin wuta tsakanin asibitin da kamfanin rarraba wutar lantarki ta Kano (KEDCO).

Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, ya kawo aikin da darajarsa ta kai sama da Naira biliyan 12.

Hon. Bichi ya ce wannan aikin wani ɓangare ne na shirin “Renewed Hope” na Shugabam ƙasa Bola Tinubu na samarwa manyan makarantu da asibitocin koyarwa wutar lantarki daga hasken rana a faɗin ƙasar.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Bichi a Majalisar Wakilai, ya bayyana cewa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano shi kaɗai ya samu ayyukan da kuɗinsu suka haura Naira biliyan 26 a bana, tare da shirin saka irin wannan tsarin a Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aiki Ɗangote (ADUSTECH) da ke Wudil, da Asibitocin Murtala da na Nasarawa.

Daraktan Hukumar Kula da Makamashi ta Ƙasa (ECN), Dakta Mustapha Abdullahi, ya tabbatar da cewa aikin zai kammalu kafin ƙarshen shekarar 2025, yana mai cewa wannan shi ne na farko irin sa a Najeriya.

Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirkire-Ƙirkire, Uche Nnaji, ya jinjina wa muhimmancin aikin a shirin sabunta fata ko kuma “Renewed Hope.”

Shugaban Asibitin AKTH, Farfesa Abdulrahman Sheshe, ya bayyana cewa Asibitin na kashe sama da Naira miliyan 180 duk wata wajen biyan wutar lantarki da dizal, yana mai cewa aikin zai rage kuɗaɗen da ake kashewa da kashi 30 cikin 100, tare da tabbatar da cigaba da samun hasken wutar lantarki ba tare da yankewa ba.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal