Daga Ibrahim Muhammad
Ɗimbin al’umma ne daga sassa daban-daban suka halarci ɗaurin auren ‘ya’yan Kwamishina na ɗaya a Hukumar Amintttattu na Asusun Fansho na jihar Kano, Hon. Hassan Muhammad Amin a unguwar Chiranchi a yankin ƙaramar hukumar Gwale, Kano a safiyar ranar Asabar.
Hon.Hassan Muhammad Amin, wanda ya ba da auren ‘ya’yansa mata guda biyu; Amarya Halima Hassan Muhammad Amin (Sadiya) da angonta Umar Shitu Sharubutu da Amarya Saudat Hassan Aminu (Yesmin) da Angonta Injiniya Mahmud Amin.
Uban Amaren Hon. Hassan ya bayyana matuƙar jin daɗi da godiya ga Allah da ɗimbin mutane da suka amsa wannan gayyata tasa ta zuwa ɗaurin auren na ‘ya’yansa, wanda ƙauna ce ta jawo hakan.
Ya bayyana aure da cewa ibada mai muhimmanci, Sunna ce ta Manzon Allah da idan aka yi shi ana buƙatar haƙuri da fahimta da girmamawa da sanin ya kamata a tsaƙanin ma’auratan, da hakan zai zama wani ginshiƙi na samar da zuriyya mai cike da kyakkyawar tarbiyya.
Hon. Hassan Muhammad Amin, ya gode wa ma’aikatan Hukumar Amintttattu na Asusun Fansho ƙarƙashin jagorancin Alhaji Habu Muhammad Fagge, wanda suka sami halartar ɗaurin auren da waɗanda suka yi masa addu’a da fatan alkhairi daga nesa.
Haka kuma ya gode wa muƙarraban gwamnatin jihar Kano da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da ma’aikata da sauran al’umma maza da mata da ‘yan’uwa da abokan arziƙi da suka zo suka taya shi farin cika a wannan hidima, tare da yin addu’ar Allah ya saka wa kowa da alheri.
Mutane da dama a yayin ɗaurin auren sun bayyana cewa ba su yi mamakin irin yawan mutanen da suka halarci ɗaurin aure ba bisa la’akari da halin Hon. Hassan Muhammad Amin mutum ne mai karamci, taimako da girmama mutane.








