Daga Ibrahim Muhammad
Jaridar Madubin Arewa ta karrama shugaban kamfanin HAY Synergy Link da ke Rimin Gata a jihar Kano, Alhaji Hudu Yakub Senior Rimin Gata bisa irin gudunmwa da yake bayarwa ga bunƙasa cigaban al’umma.
A yayin taron karramawar da aka gudanar ranar Lahadi a harabar kamfanin, babban jami’in jaridar Madubin Arewa, Alhaji Ibrahim Nakogari da shi ne ya miƙa karramawar ya ce sun bai wa matashi.
Alhaji Hudu Yakub Senior Rimin Gata, wannan karramawa ne, don karfafa masa gwiwa a kan irin kishinsa da suka gani ga cigaban al’umma.
Ya ce bisa la’akari da yadda yake bai wa mutane da dama aikin yi a ɓangarorin harkokinsa da yake tun daga kan masu tukin motoci da kuma ɓangaren gine-ginen gidaje da yake domin masu karamin ƙarfi su mallaka, cikin rahusa da bai wa matasa aiki a ɓangarori na kamfanin suka ga cancantar karrama shi.
Ya cewa mutane masu ɗimbin yawa ne ke amfana da shi ta aiki da suke a ƙarƙashinsa hakan ba ƙaramar gudunmuwa yake bai wa cigaban al’umma ba, musamman idan aka yi duba da yadda rayuwa ta yi tsada da yadda ake kuma fama da ƙarancin ayyukan yi.
Alhaji Ibrahim Nakogari ya ce domin fito da wannan abin alkhairi da yake duniya ta sani a kuma yi koyi da shi tasa jaridar ta karrama shi domin ta ƙara masa azama kan abin da yake kuma wasu ma su yi koyi da shi.
A jawabinsa bayan karɓar shaidar karrama shi da jaridar Madubin Arewa ta yi, Shugaban kamfanin na HAY Synergy Link, Alhaji Hudu Yakub Rimin Gata ya ja hankalin matasa ‘yan’uwansa a kan su guji zaman banza su rungumi sana’a komai ƙanƙantar ta, kuma su tsare gaskiya da amana za su ga fa’idar hakan a cigaban rayuwarsu.
Ya yi nuni da cewa yanzu haka ƙarƙashin kamfanin nasa tsakanin direbobi da yaran mota da bakanikai suna da ma’aikata da suka kai mutum 200 ban da sauran ɓangarori da su ma suke da ma’aikata kuma sirrin wannan cigaba da nasara da suke samu shi ne na riƙo da gaskiya da amana da suke.
Alhaji Hudu Yakub Senior Rimin Gata ya nuna mutuƙar jin daɗi da godiya ga jaridar da ta hango irin gudunmawa da suke bayarwa har ta karrama shi, ya kuma gode wa abokan hulɗar sa da mutane da suke ba su amanar kula da dukiyarsu Allah kuma yake sanya mata albarka a harkokin da suke gudanarwa.
Alhaji Hudu Yakub Senior Rimin Gata ya ce a ɓangaren gwamnati ma suna ba da gudunmuwa wajen biyan haraji kashi daban-daban tun daga matakin na ƙaramar hukuma da gwamnatin jiha da tarayya sai dai ya ja hankalin gwamnati a kan a riƙa ba su gudunmuwa ta sassauta musu kuɗin haraji domin ƙarfafa musu gwiwa wajen gudunmawa da suke bayarwa na samar da ayyuka a tsakanin al’umma.
Daya daga cikin aminan Alhaji Hudu Yakub da ya halarci karramawar Ibrahim Malam Hudu ya ce wanda aka karrama mutum ne mai hazaƙa da ƙoƙarin riƙe gaskiya da amana na abokan hulɗarsa yana ba da gudunmuwa ga samar da aiki ga mutane domin akwai ma’aikata sama da 400 da ke aiki a ƙarƙashinsa ga shi kuma da tausayi ne da yawan taimako da son yaga na ƙasa ya ɗago.






