Daga Ibrahim Muhammad
Jihar Kano ta fito a matsayin jiha ta fi kowa cin jarabawar kammala Sakandare ta cikin gida (SSCE Internal) ta shekarar 2025 wacce Hukumar Jarabawa ta Ƙasa (NECO) ta gudanar.
Wannan gagarumar nasara ta samo asali ne daga manyan gyare-gyaren da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar tare da ci gaba da inganta ilimi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, Shugaban NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi, ya bayyana cewa daga cikin ɗalibai 1,358,339 da suka zauna jarabawar a Yuni/Julai, ɗalibai 818,492, wanda yake daidai da kashi 60.26 cikin 100, sun samu darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Haka kuma, ɗalibai 1,144,496, wanda yake daidai da kashi 84.26 cikin 100, sun samu darussa biyar da suka wuce, ba tare da la’akari da waɗannan darussa biyu ba.
Kano ce ta jagoranci ƙasa da ɗalibai 68,159 (kashi 5.020 cikin 100 na jimillar ɗaliban ƙasa) suka samu darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi. Lagos ta biyo baya da ɗalibai 67,007 (kashi 4.930 cikin 100), yayin da Oyo ta zo ta uku da ɗalibai 48,742.
Wannan nasarar tarihi ta nuna sakamakon shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf mai kishin ilimi, wanda a koyaushe ya sanya kuɗi, gina makarantu, da kuma bunƙasa samun damar ilimi a sahun gaba cikin ayyukan gwamnatinsa.
A cikin kasafin kuɗin 2024 da 2025, ɓangaren ilimi ne ya samu kaso mafi tsoka, abin da ya bai wa gwamnatin damar gudanar da manyan gyare-gyare da suka farfaɗo da makarantu, tare da mayar da ƙarfin gwiwa ga ilimi a matsayin muhimmin ɓangaren da gwamnati ke bai wa muhimmanci.








