Daga Ibrahim Muhammad
Ƙaramin ministan gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu ya yi wa jihar Kano komai na ba ta kulawa na musamman a wannan mulki da yake.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi bayan karrama shi da ƙungiyar Progressive APC Alliance Forum (PAAF) ta yi a yayin taron ƙaddamar da shugabanninta na jihar Kano da na matakin wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar.
Ya ƙara da cewa jihar Kano ta amfana da ɗimbin muƙamai da shugaban ƙasa ya ba iwa ‘yan asalin jihar a ɓangarori daban-daban da shi ma yana daga cikin wanda ya amfana, kuma ana kawo ayyuka na cigaba daga gwamnatin tarayya.
Hon. Ata ya ce saboda haka za su mara wa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu ya sami nasara ta ɗorawa a kan cigaba da mulkinsa a zaɓe mai zuwa na 2027, sannan kuma ya ƙara da bayyana goyon bayansa ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa na ƙasa Sanata Barau I Jibrin a matsayin wanda zai yi takara a ƙarƙashin jam’iyyarsu ta APC a jihar Kano a 2027 idan aka yi la’akari da gudunmawa da yake bayarwa wajen bunƙasa cigaban jihar Kano da kuma hidimtawa jam’iyyar APC.
Ministan ya gode wa ƙungiyar ta PAAF bisa wannan karramawar da ta yi masa da kuma jinjina musu bisa ƙoƙarin da suke na nuna goyon bayansu ga shugaba ƙasa Bola Ahmad Tunibu ya zarce da kuma goyon bayan mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibrin a matsayin wanda suke son ya yi takarar Gwamnan Kano a zaɓe mai zuwa 2027.
Shi ma a nasa jawabin, ɗaya daga cikin waɗanda ƙungiyar ta PAAF ta karrama a yayin taron, tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Wudil da Garko, Injiniya Ali Wudil ya yaba musu bisa yadda suka kalli irin hidima da shugaban ƙasa yake wa ƙasar nan musamman jihar Kano suka nuna goyon baya kan ya zarce da kuma jagoransu Sanata Barau I Jibrin Sanatan Kano ta Arewa mataimakin shugaban majalisar Dattawa a kan ya nemi Gwamnan Kano.
Injiniya Ali Wudil ya kuma nuna jin daɗinsa da PAAP ɗin ta karrama su domin gamsuwa da yadda suke jagoranci.
Ya yi fatan Allah ya tabbatar da alheri ga ƙungiyar kuma za su cigaba da ba da kowace irin gudunmawa ƙofarsu a buɗe take kan hakan kamar yadda dama suke yi daidai gwargwado.
Injiniya Ali Wudil ya yi nuni da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu shi ne ya naɗa Farfesa Ma’aji shugaban Hukumar Cigaban Arewa maso Yamma, wanda ɗan Kano ne shi ma ya naɗa shi ya wakilci Kano a Hukumar, sannan ya ɗauki ma hedikwatar Hukumar gaba ɗaya ya kawo ta jihar Kano ta silar Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Barau I. Jibrin Maliya don haka za su ba da goyon na abin da Allah ya hore musu za su taimaka wa Tinubu don ya koma mulkin ƙasar nan karo na biyu a 2027.







