Kwankwaso Da Abba Gida-Gida Za Su Koma APC?

Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya je sasanta da Kwankwaso da duk wasu mutanen da ke shirin shiga jam’iyyar.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Kano kwanaki kadan bayan hukuncin kotun koli da ta tabbatar da zaben Abba Yusuf (Abba Gida-Gida) a matsayin gwamnan jihar Kano.

Shugaban ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar da su bi hanyar tattaunawa da daidaikun jama’a, kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa da ke shirye su shigo jam’iyyar domin bunkasa hadin kai, ci gaba da ci gaban jihar. Umurnin da shugaban ya bayar ya bai wa dukkan masu ruwa da tsaki da suka halarci taron mamaki, yayin da suka sha alwashin bin umarnin shugaban.

Wata majiya a wajen taron ta shaida wa POLITICS DIGEST cewa tuni aka mika wannan kiran ga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP ciki har da gwamna, kuma sun nuna sha’awarsu ta shiga jam’iyyar APC, amma sun nemi a ba su karin lokaci domin tuntubar shugabansu na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Tayin da aka bai wa jam’iyyar NNPP kashi 50% na shugabancin jam’iyyar tun daga matakin unguwanni da kananan hukumomi da jiha.

An kuma bukaci gwamnan da ya kara nade-nade domin shigar da ’yan jam’iyyar APC na asali a cikin gwamnatin tasa.

Ba a tabbatar ko gwamnan da ubangidansa Sanata Kwankwaso za su amince da wannan tayin da gwamnatin Bola Ahmad Tinibu ya yi masu.

Wadanda suka halarci taron masu ruwa da tsakin sun hada da mataimakin shugaban majalisar Dattawa Barau Jibrin, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a 2023; Nasiru Yusuf Gawuna, karamin ministan gidaje da raya birane; Abdullahi Gwarzo, karamar ministar babban birnin tarayya; Mariya Mahmoud Bunkure da tsohon shugaban majalisar wakilai; Alhassan Ado Doguwa da sauransu.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano