Daga Ibrahim Muhammad
Al’umma daga ƙananan hukumomin Madobi da Bichi sun raka sabon Manajan Daraktan Hukumar Kogunan Haɗejia da Jama’are, tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi da tsohon Kwamishina, Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso sabon babban Daraktan kuɗi da mulki a Hukumar da bayan naɗin da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa mutum biyar sabbin muƙamai a Hukumar.
A ranar Talata ne sabbin shugabannin suka kama aiki bayan da masoya da magoya bayansu suka yi musu rakiya ta musamman domin shaida yadda za su kama aikin.
A jawabin sabon shugaban Hukumar, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ya yi alƙawari ga al’ummar jihohin Kano Jigawa da Bauchi na inganta harkokin noma da kuma samar da aikin yi ga ɗimbin matasa kasancewar Ma’aikatar babba ce, za su yi amfani da ita wajen tallafa wa ‘yan jam’iyyar APC, za su zo da tsare-tsaren da tallafi da zai kai ga kowa.
Sabon Manajan Daraktan na Hukumar Kogunan Haɗejia da Jama’are, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ya ce akwai tsare-tsare na noman zamanin da zai kyautata shi da za a riƙa yin nuna a gida, kuma a riƙa yin fiye da sau biyu a shekara da hakan zai amfani masu ƙaramin ƙarfi, kuma ya haɓɓaka tattalin arziƙi.
Ya nemi haɗin kai da goyon bayan ma’aikatan Hukumar da sauran al’umma ta yadda za a haɗu a ciyar da Ma’aikatar gaba yadda za ta amfani al’umma.
Sannan ya gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa ba su wannan damar da aka yi.
A nasa jawabin, Babban Daraktan Kuɗi da Mulki na Hukumar, Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce, zai yi ƙoƙari don inganta rayuwar al’ummar jihohin Kano Jigawa da Bauchi.
Ya kuma gode wa masoya da magoya baya da suka rako su Ma’aikatar domin kama aiki. Ya ba da tabbacin za su ɓullo da tsare-tsare na kyautata wa magoya baya sosai.
Sannan ya yi kira da a taya su da addu’ar Allah ya ba su ikon sauke nauyin da shugaban ƙasa ya ɗora musu.






