Sat. May 10th, 2025

Kyakkyawar Manufa Ke Sa Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Samun Lambar Yabo -Hon. Ibrahim Ali Namadi

By Saleh Aliyu Apr 15, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Kwamishinan Ma’aikatar Sufuri na jihar Kano, Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala, ya bayyana cewa aiki tuƙuru da kyakkyawan niyya na son ci gaban al’ummar jihar Kano ne ke jagorantar Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake ta samun lambobin karramawar daga wurare daban-daban.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida. Ya kuma nuna farin cikinsa da irin tarin lambobin yabo da yake Gwamna Abba Kabir Yusuf yake samu, ciki har ta Gwamna mafi fice a fannin kula da ilimi a Nijeriya.

Ya ce hakan ya samu ne ta hanyar nazartar kyakkyawan jagoranci da jaridun LEADERSHIP da VANGUARD da kuma wadda ‘ya ƙasar Maroko suka ba shi suka yi.

Ya ce wannan karramawar ta cancance shi idan aka yi la’akari da sadaukarwar da yake na jagoranci nagari, da jajircewarsa wajen ci gaban ilimi da sauran fannoni daban-daban a jihar Kano.

Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala ya yi nuni da cewa a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf jihar Kano an samu cigaba sosai wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa da kyautata harkar lafiya da sufuri da biyan ma’aikata da ‘yan fansho haƙƙoƙinsu ba tare da jinkiri ba.

Hon. Namadi ya jaddada goyon bayansa ga irin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake yi, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, bunƙasa rayuwar matasa, da bunƙasa harkar kasuwanci da sufuri a faɗin jihar Kano.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *