Ma’aikatar Ƙwadago Ta Tarayya Ta Yi Taro Kan Sanin Makamar Aiki A Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kwanturola mai kula da ofishin jihar Kano na Ma’aikatar Ƙwadago ta Tarayya, Alhaji Abdullahi Aliyu, ya bayyana cewa lokuci zuwa lokaci suna shirya taro don ƙara bayyana irin yanayin ayyukansu da abokan ayyukansu kamfanoni wani lokaci da gwamnatoci don ƙara fahimtar juna da zaman lafiya tsakani.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron da suka gudanar da masu kamfanoni da ma’aikata a ranar Asabar ya ce, su na taron ne
don tabbatar da masu kamfani suna bin doka da kula da rayuwar ma’aikata yadda ya kamata da ba su haƙƙoƙinsu, su kuma ma’aikata ya zama suna bin ƙa’idodi na aiki da yin abin da ya kamata hakan shi zai haifar da zaman lafiya tsakaninsu. Ya ƙara da cewa ita gwamnatin tarayya da duk wata hukuma ma, abin da tasa a gaba kafin komai shi ne zaman lafiya, wanda yana da muhimmanci kamfanoni da abokan hulda ma’aikata ya zamanto sun zaune lafiya shi ne zai kawo cigaba.

Ya yi nuni da cewa ba a hana ɗan’adam yin kuka ba, illa dai duk yadda ka kai da ƙoƙarin yin gyara wani wajen ma idonka ba zai kai ba, balle ka yi wani abu, amma suna yin iya ƙoƙarinsu su tabbatar haƙƙoƙin da gwamnati ta ɗora musu sun bi, waɗanda haƙƙi ke wuyansu suna faɗakar da su, suna kuma biyayar su tabbatar suna bin dokokin, wani lokaci suna nasara a bi wani lokacin kuma sai dai a yi haƙuri.

Ya ce mahalarta taron yawanci manajoji ne na kamfanoni da ƙananan ma’aikata da matsakaita da manya ana haɗa su tare ne saboda in kana so ka tabbatar da nasarar abu ka hada kowa, shi ƙaramin ma’aikaci idan yana da ƙorafi wani lokaci yana neman inda zai faɗa ne, in ka yi nasarar haɗa shi da babban ma’aikaci in ya yi ƙorafi a inda yake ganin yana da damar ya yi ko ba ka gayawa babban ma’aikacin ga ƙorafin ba, to wata dama ce da babban ma’aikaci zai san ashe wani abu yana faruwa, kuma a wajen za su ji
saboda ko da sun je ‘inspection’ ba sa ganin matsala in ba an haɗu a irin wannan taro ba. “Sai mu gaya musu ga abin da yake na doka da shi ma’aikaci bai sani ba.

Alhaji Abdullahi Aliyu ya ce yin wannan taron ana ilmantar da masu kamfani da ma’aikata da janyo hankulansu lallai su bi doka ta jan hankalinsu “persuasion” da shawarwari don a cimma nasara tare, duk mai kamfani idan ya kyautata wa ma’aikata kan shi ya kyautatawa, domin su ma za su kyautata masa, in bai kyautata musu ba illar da za ta auku ga kamfanonin shi ma ba zai ji daɗinsa ba, suna ƙoƙarin kowane ɓangare su ba su shawarwari da za su kyautatawa juna.

Ya ce irin wannan taro suna tattara matsaloli su rubuta rahoto su aika hedikwatar domin a ɗauki mataki da za a sa a doka dan kyautata tsarin tafiyar da harkar kwadago tsakanin kamfani da ma’aikata taron kuma na haɗin gwiwa ne tsakaninsu da kamfanoni da ake gabatar da shi don amfanar da su kamfanin da masu aikin da gwamnati, wanda ita ribar ta taga kasa ta zauna lafiya da samun cigaba na tattalin arziƙi su kuma masu kamfani suna yi ne don riba don su taimaka wa ƙasa ta cigaba a samar da aikin yi shi, kuma ma’aikaci yana yi ne don shi ma ya amfanar da iyalinsa ya kyautatawa harkokin rayuwarsa.

Da yake ƙarin haske game da da taron, ɗaya daga jami’an Ma’aikatar Ƙwadago ta Tarayya, Murtala Haruna Abdullahi na sahun kula da kamfanoni “factory inspector” ya ce suna shirya taron ne domin faɗakarwa, horarwa da ƙarawa juna sani ta yadda masu ɗaukar ma’aikata da ma’aikata a musamman a masana’antu da sauran wuraren aiki za su kasance a wayar musu da kai kan yadda za su yi aiki tare da kyautatawa a tsakaninsu yadda doka ta tanada.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?