Magidanci Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Ɗauki Wayarsa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta ce ta kama wani magidanc mai shekara 33, mai suna Ibrahim Abubakar, mazaunin Sabon Gari a karamar hukumar Girei, bisa zargin kashe matarsa mai shekara 25, mai suna Hajara Sa’adu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahya Nguroje ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Nguroje ya ce bayan samun korafi daga wajen mahaifin marigayiyar ce kan abin da ya faru, nan take suka kama mijin nata.

Nguroje ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsa da shi, kuma ya ce ya kashe matar tasa ne bayan daukar wayarsa da ta yi.

“An same ta kwance cikin jini, sai aka tafi da ita zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta,” in ji Nguroje.

Ya kara da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike da kuma tattara hujjoji, kafin gurfanar da shi gaban kotu.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano