Daga Ibrahim Muhammad
Majalisar Hafizan Alƙur’ani mai girma ta Nijeriya ƙarƙashin shugabanta, garkuwan Alƙur’ani, Malam Yusuf Hamza Yusuf Abu Abdul Majid, sun gudanar da saukar karatun Alƙur’ani mai girma na adadin sauka mai yawa ga Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan kammala addu’o’in da ya jagoranta, Alaramma Hamza Yusuf Hamza Abu Abdul Majid ya ce, sun ji wannan rashi a jikinsu ba a Kano kawai da Nijeriya aka yi wa ba duniya aka yi wa.
Ya ce gudunmawar da Alhaji Aminu Ɗantata ya bayar a duniya ba za ta ƙirgu ba. “Shi mutumin kirki ne mai ƙaunar Allah da Manzonsa, ya ba da gudunmawa ta kowane ɓangare, harkar ilimi, kasuwanci, lafiya, addini da kyautata zumunci. Muna fatan Allah ya karɓi ayyukansa da yardar Allah,” in ji shi.
Ya ce duniya ma shaida ce cewa Alhaji Aminu Ɗantata mutumin kirki ne, kuma Allah ya cika masa burinsa, dama babban burinsa a binne shi a Madina birnin Annabi, kuma Allah ya cika masa buri, kuma ya bar ‘ya’ya masu albarka magada shi ma mahaifinsa ya gada mutumin kirki ne ya gaji kirkisa.
Ya ce, “Irin alheri da ya yi da muke alfahari da su irin su Jami’ar Musulunci ta Katsina a shekara 20 baya ya ba da gudunmawar Naira miliyan 1000, kamar yanzu a ce an ba da Tiriliyan ɗaya ne. A wata Jami’ar ma ya ba da sama da haka, kuma akwai abin da ba ya ma son kowa ya sani, masallacin Jami’a ma na Bayero tsohuwa shi ya gina, kaso 70 ya bayar, Shaikh Isyaka Rabiu ya bayar da 30. Ayyukansa ba za su ƙirgu ba.
“Babban abin da ake masa shaida da shi shi ne gudun riya, ba ya son ya yi abu ya faɗa. Tsakaninsa da Allah yake. Mutumin kirki ne, ya sami kyakkyawan shaida,” Garkuwar Alkur’ani ya bayyana.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi a kan su sani yin abu domin Allah irin yadda Aminu Ɗantata yake su yi ƙoƙari su riƙa taimaka wa bayin Allah domin shi dukiyarsa Allah ya sa mata albarka, yana tsarkake ta ba ta jin ɗiba da kisa, idan ya kashe dubu, sai miliyan ta shigo, aikinsa ke nan. “Har ya koma ga Allah ya ma daina neman kuɗi, ,sune ma suke neman sa, kuma ya nuna duniyar ma ta ishe shi, so yake ya je ya haɗu da magabatansa da masoyansa saboda ya san shi yana neman yardar Allah ne ba yana neman ya cigaba da zama a duniya ba ne,” ya tabbatar.
Malam Yusuf Hamza Yusuf Abu Abdul Majid Garkuwan Hafizan Alƙur’ani ya ce bai taɓa ganin mai arziƙin da yake raye ba ya burin Allah ya ƙara masa lokaci ya ci gaba da rayuwa a duniya ba irin Aminu Ɗantata ba, ya shirya wa tafiya lahira, kuma ya tafi a cikin aminci da yardar Allah.






