Daga Ibrahim Muhammad
Ƙungiyar makarantun Islamiyya na jihar Kano ta naɗa Zannan Kwankwasiyya, Ambasada Abubakar Yahuza Gama a matsayin Maji Daɗin makarantun Islamiyya na jihar Kano sakamakon ɗimbin gudunmuwa da yake bayarwa ga cigaban makarantun.
An gudanar da naɗin ne a yayin taron Mauludeen Nabiyyi (s) da ƙungiyar makarantun ta saba gudawa duk shekara da aka yi a filin wasan ƙwallon na Sabon Gari ranar Lahadi.
A jawabinsa bayan naɗin zannan Kwankwasiyya ya bayyana naɗin da ƙungiyar makarantun Islamiyya ta yi masa na Maji Daɗin makarantun Islamiyya da cewa ya zama abin tarihi gare shi domin duk shekara suna zuwa wannan taro da na bana an karrama shi yanzu yana bayani ba da hula ba da rawani da aka yi masa naɗi ya gode wa Allah da wannan karramawa da aka yi masa wanda shi ma yana ganin mai iya karrama duk wanda zai taimakawa wajen hidimtawa makarantun Islamiyya ne.
Ya ƙara da bayyana cewa ƙungiyar makarantun Islamiyya sama da shekaru da dama yana hidima a cikinta tun yana lokacin yana kawo ɗalibansu wajen maulidin, sai ya ga ana buƙatar ƙarin kyaututtuka da yawa ga makarantun tun daga wancan lokacin ya ake inganta maulidin da kawo abubuwa za su taimakawa don kyautatawa cigaban makarantun Islamiyya.
Ya nuni da yanzu gwamnatin jihar kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ana ta gyaran makarantun Firamare da Sakandire har da na Islamiyya za su kuma cigaba jawo da haɗa kai da gwamnati wajen inganta da bunƙasa makarantun Islamiyya da suke fatan kuma sauran shugabanni da masu hali su zo a riƙa taimakawa.
A cikin jawabin nasa Maji Daɗin makarantun Islamiyya na jihar Kano Zannan Kwankwasiyya ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin hidimar ɗaliban makarantun Islamiyya domin a yi musu rijistar katin zaɓe tun daga wanda ake ta waya da kwamfuta inda za su je su karɓa duba da yin katin zaɓen na da muhimmanci idan zaɓen yazo akwai wanda zaka ga zai taimake ka kuma idan ba ka da rijistar zaɓe ba yadda za ka yi ka zaɓe shi, don haka zai ɗauki nauyin ɗalibai na makarantun da suka cancanci yin rijistar don tabbatar da an yi musu.
Shi ma Dakta MD Hasan, wanda ya taɓa neman tsayawa takarar shugaban karamar hukumar Nasarawa ya ce suna godiya ga Allah da ganin wannan rana da dama taro ne da suka gada aka saba gudanarwa na Maulidi tun iyaye da kakanni, sun taso ne sun ga ana yi duk lokacin da watan maulidi ya zo mutane kan fito su nuna murna da haihuwar Manzon Allah (s).
MD ya ce ba za su manta da wannan rana ba a rayuwarsu za su cigaba da raya shi da nuna wa ƙanne da ‘ya’ya su cigaba da rayawa, kuma karrama Zannan Kwankwasiyya da aka yi da Maji Daɗin makarantun Islamiyya an ajiye ƙwarya a gurbinta.
Alhaji Abubakar Yahuza Gama duk wanda ya san shi ya san daga ina yake hidimar addini ina za ka hidimar addini suna fata Allah ya taya shi riƙo.
Kansilan mazaɓar Gama. Hon. Abdulkarim Ibrahim Gama da shi ma ya halarci taron ya ce a shirye suke su bai wa ƙungiyar shawarwari da wuce mata gaba domin samun cin gajiyar gwamnati da kuma kawo gudunmawa ga cigabanta ya yaba wa ƙungiyar makarantun Islamiyyar kan gudunmuwa da take bayarwa da nuna jin daɗinsa da karrama jagoransu Zannan Kwakwasiyya da koyaushe yake bayar da gudunmuwa a bunƙasa cigaban makarantun Islamiyya da sauran harkoki na rayuwar al’umma.
Alhaji Muhammadu Nation Gama ɗaya da mutane da ke bayar da gudunmuwa ga cigaban al’umma yayin taron ya bayyana maulidin makarantun Islamiyya da cewa abu ne mai muhimmanci da ake karrama ɗalibai da kyautuka da hakan na ƙarawa yara masu tasowa ƙarfin gwiwa kuma irin wannan taron shi ake so don ana ƙarfafa matasa su taimaki addini.
Alhaji Mamman Nation ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta ƙara ƙaimi wajen bai wa makarantun Islamiyya kulawa ta shigowa ana irin wannan taro da ita hakan zai ba matasa ƙarfin gwiwa, su dage kan koyarwar addini.
Sannan su kuma iyaye ya ja hankalinsu su riƙa sawa yara suna zuwa makaranta don shi ne gata ɗaya da za a yi musu mafi muhimmanci in sun girma ya haska musu rayuwa.
A jawabinsa shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya na jihar Kano, Alhaji Auwal Mu’azu ya yi godiya ga Allah da ganin
taron Mauludeen da ƙungiyar ta saba yi duk shekara da ba na shi ne karo na 46 a tarihin ta tun daga iyaye da magabatansu da suka assasa.
Ya ce Maulidin ɗaya ne daga ayyukan ƙungiyar bayan wannan akwai tarurruka na karawa juna sani da suke a tsakanin makarantun Islamiyya da suke daga lokaci zuwa lokaci da musabaƙa da sauran gasa tsakanin tsakanin ɗalibai domin zaburarwa da wa’azi da tarurruka masu munasaba da addini da suka haɗa da taron sabuwar shekarar Musulunci da maraba da Ramadan da goron Sallah.
Alhaji Mu’azu ya ce naɗin da aka yi wa Alhaji Abubakar Yahuza Gama ya biyo bayan godiya ga irin hidima da yake yi wa makarantun Islamiyya ne a jihar Kano ta fannoni da dama kuma suna fatan duk wanda ke taimaka wa ƙungiyar shekara 46 zuwa yau Allah ya saka musu da alheri.
A yayin taron an raba kyautuka ga ɗalibai da suka yi nasara a musabaƙa daban-daban da aka gudanar sannan zannan Kwankwasiyya Maji Daɗin makarantun Islamiyya na jihar Kano, Ambasada Alhaji Abubakar Yahuza Gama ya miƙa kyautar kujeru da ya samar ga wasu makarantun Islamiyya da kuma da cika alƙawarin tallafi da yayi musu.






