Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana makarantu masu zaman kansu suna mutuƙar bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban ilimi domin gwamnati kaɗai ba za ta iya gamsar da ba da ilimi ga al’umma gaba ɗaya ba, musamman a matakin farko na Firamare da ƙaramar Sakandire ba.
Tsohon Kwamishinan Ayyuka Gidaje da Sufuri
na juhar Kano, Hon. Aminu Aliyu Wadil ne ya bayyana hakan a taron yaye ɗalibai da raba kyautuka na makarantar ‘Yan Dutse.
Ya ce dole makarantu masu zaman kansu ne za su cike wannnan giɓin, kuma gwamnatoci sun ba da yanayi mai kyau ga makarantun, su ma makarantu masu zaman kansu sun karɓi ƙalubalen da gwamnati ta yi musu ana samun cigaba, duk da dai ba a rasa ‘yan abubuwa na ƙalubale, amma akwai Hukuma ta musamman da take kula da sa ido ga makarantun don kiyaye doka da tarbiyya don a sami ingantaccen ilimi.
Hon. Injiniya Aminu Aliyu Wadil ya ce a matsayinsa na ɗan ƙasa yana ganin ƙoƙarin da Majalisun Ƙasa suke na yin doka na lallai duk ma’aikatun gwamnati sai sun sanya ‘ya’yansu a makarantun gwamnati yana ganin hakan ya faru ne saboda taɓarɓarewar makarantu mallakar gwamnati.
Tsohon Kwamishina a jihar Kano, Hon. Amin Aliyu Wadil ya bayyana cewa makarantar ‘yan Dutse koyaushe tana yaye ɗalibai managarta domin yana da yara guda shida a makarantar, wasu sun gama suna Jami’a, wasu har sun yi aure.
Hon. Injiniya Aminu Aliyu Wadil ya yadda makarantar ke shirya taron yaye ɗalibai da raba kyautuka, wannan ya nuna irin ƙoƙarin iyaye da ƙwazon malamai shi ya sa ma suka zo makarantar don halartar wannan taro don gamsuwa da abubuwa da ake.






