Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana cewa an sami gagarumar nasara da habɓakar cigaban kasuwar hada-hadar wayoyi ta Farm Centre a ƙarƙashin jagorancin zaɓaɓɓen shugaban kasuwar, Ambasada Jamilu Bala Gama.
Da yake zantawa da ‘yan jarida, shugaban kasuwar ya bayyana cewa a cikin kwanaki sama da 90 daga zaɓen
su a kan shugabanci sun sami nasarar da ko a shekara ɗaya aka ce an samu ba ƙaramin cigaba ba ne, domin sun zo sun sami kasuwar shara ma kawai ta mamaye titunanta, har gwamnati ta yi ƙorafi a kai, amma zuwan su shugabanci suka sa ake kwashewa da kuma yi wa masu sharar albashi yanzu babu inda shara ke taruwa.
Ya ce sannan sun tarar da masu gadi da ba su wuce mutum 40 ba, suka ƙara yawansu zuwa 91 aka ƙara musu yawan albashi daga N25,000 zuwa 30,000 don inganta tsaro da kafa doka ta hana mata kai wa dare a cikin kasuwar da hana duk wani abu da bai kamata ba.
Ambasada Jamilu Bala Gama ya ce kullum a matsayinsu na shugabanni suna karɓar ƙorafe-ƙorafe a tsakani ‘yan kasuwar da yin sulhu da daidaita tsakani sama da 100 su yi sasanci wani abin ma sai an kai shi wajen ‘yan sanda, sannan a dawo a warware a ofishin kasuwa wani ma sai an je kotu a sake dawowa a sasanta a sami maslaha.
Ya ƙara da nuna cewa suna da tsari na ajiye duk wani bayani na abubuwa da ke faruwa a kasuwar, don haka ma suka ware sashe guda da ofis na babban jami’in tsaro a kasuwar da suke kula da matsaloli su tattara bayanai a kawowa shugabanni don a ga yadda za a warware matsalolin.
Ambasada Jamilu ya ce suna da matasa masu rijista ‘yan kasuwar sama da 21,000 a kwanciyarsu dattawa ba su da yawa. “Duk matsaloli da suka taso suna ƙoƙarin ɗora su a kan kyakkyawar hanya. Akwai dokoki da muka sa don tsaftace harkar wayoyin daga bata-gari an sa dokar kar a sayi waya sai da resit da kwalinta na ainihi, in aka saya a kan wannan ƙa’ida duk matsala da za ta iya tasowa za ta zo da sauƙi.
“Yanzu irin matsaloli da ake samu a baya kamar guda 100 a kullum yanzu bai wuce a samu 10 ba. Duk sun magantarsu cikin ikon Allah,” in ji shi.
Shugaban kasuwar waya ta Farm Centre ya ce, “Babu wani da yake yin wani abu a zahiri da ya sabawa doka a kasuwar domin tun kafin ya zama shugaban kasuwar yana matsayin sakatare an haɗu da jami’an tsaro an yi doka na hana canza IME, kuma ‘yan kasuwar masu bin doka ne da kiyaye ta.
Ambasada Jamilu Bala Gama ya ce a kasuwar ta Farm Centre yawan adadin mutane da suke gudanar da sana’o’i a cikinta yawansu ya fi na ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da ba su wuce 70,000 ba, amma a kasuwar akwai mutane sama da 100,000 don haka sai dai gwamnati ta yaba musu bisa nauyi da suka rage mata na samar da aikin yi ga matasa.
Ya ce matasa masu harkoki a kasuwar sama da 21,000 kowanne akwai wasu a ƙasansa za a sami sama da mutane 200,000 da suke gudanar da sana’a a cikin kasuwar, kuma su shugabannin kasuwar suna da kyakkyawar alaƙa da gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro.
Ambasada Jamilu Bala Gama ya ce yanzu a kasuwar suna da manyan Plaza guda 18 da ake harkoki a ciki da wasu guda biyar da ba a ƙarasa ginin su ba, amma a haka mutane da yawa ba su da wuri.
“Don haka muna kira ga gwamnatin jihar Kano ta Abba Kabir Yusuf ta kawo mana taimako don a ƙara faɗada kasuwar. Akwai wurare da muka ware muke so a gina kwantenoni guda 1000 da kuma wuri na gwamnati da suke so a gina kasuwa da za ta ɗauki mutane 2000. Wannan zai taimaka wajen ƙara samar da wuraren da za mu sama wa al’umma aiki don ragewa gwamnati nauyi,” ya bayyana.






