Manoma zasu amfana da tallafin $25, 000 a Nasarawa

Daga Zubairu Lawal Lafai

Kungiyoyin Manoma a jihar Nasarawa zasu amfana da tallafin dalan Amurka 25,000 domin bunqasa harkan Noma a fadin jihar.

Da yake jawabi Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule yace; Bankin Duniya tayi alkawarin baiwa al’umomin dake kauyaka goma tallafi domin gudanar da aikin gona da samar da wadacecen abinchi.

Yace; kauyuka guda goma dake jihar Nasarawa da zasu amfana da wannan tallafin sun hada da manoman dake karamar Hukumar Doma da na karamar Hukumar Toto.

Gwamnan ya bayyana hakane a lokacin da yakewa manoma jawabi a ziyarar da yakai garin Doma.

Gwamnan yace; kuddurin Gwamnatinsa na ganin jihar Nasarawa ta yiwa sauran jihohi fincin kau wajen samar da wadacecen abinchi mai gina jiki a Nijariya yasa.

A makon da ya gabata Gwamnatinsa ta rabawa manoma motochin noma guda 23 da tallafin kudi naira dubu goma ga dumbin manoma domin karfafa masu giwa.

Gwamnan yace yana tare da kungiyoyin manoma a koda yaushe. Kuma Gwamnati tana samar da abubuwan more rayuwa ga kananan manoma a jihar.

Ya Qara da cewa jajurcewar da Gwamnatinsa keyi wajen ganin manoma sun tsayu da kafafunsu, gashi Bankin Duniya tare da hadin giwar Bankin raya harkan noma ta Afirka da Gwamnatin jihar sukaga cancantar manoman jihar Nasarawa aka fara basu wannan tallafin na &25,000 ga ko wani kauye har kauyuka goma.

Shima a nasa jawabin Shugaban Kungiyar ACReSAL Dr. Joy Iganya Agene yace; kimanin manoma 620 ne zasu amfana da tallafin wannan kudin domin bunqasa harkan noma a jihar Nasarawa.

Yace; shirin ya hada maza da mata bai ware wasu jinsin ba. A madadin haka mata kimanin 367 ne zasu amfana da wannan tallafin.

Maza kimanin 253 ne zasu amfana da wannan tallafin .

Shima a nasa jawabin Sarkin Doma Alihaji Aliyu Ogah (Andoma na Doma) yayi godiya da Gwamna Abdullahi Sule dake samar da kuddurin cigaban al’umman jihar Nasarawa a koda yaushe.

Sarkin yayi kira ga al’umman karamar Hukumar Toto da Doma da zasu ci gajiyar wannan tallafin dasu zage dantse su yi amfani da kudaden ta anyar noma da al’umman Qasa zasu amfana.

Sannan yayi godiya ga wadanan kungiyoyin dama Bankin Duniya da ya tallafima al’umman jihar.

Related Posts

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun