Matasan Arewa Family Ya Yaye Matasa 460 Da Aka Koya Wa Sana’o’i Na Dogaro Da Kai

Daga Ibrahim Muhammad

Matasan Arewa Family ta gudanar da taron yaye ɗalibai maza da mata da aka koyawa sana’o’i daban-daban domin ɗora su a kan tafarkin dogaro da kai a ƙaramar hukumar Nasarawa ranar Lahadi.

Muhammad Mubarak, wanda yake jagorantar horar da matasa a ƙarƙashin Matasan Arewa Family, kuma shi ne darakta na makarantar FACES SCIENCE AND TECHNOLOGY ya ce, duba da yanayi da ƙasa take ciki a yanzu na rashin ayyuka musamman a tsakanin matasa maza da mata shi ya sa suka duba akwai ayyuka na sana’o’i da ya kamata matasa su riƙa yi na hannu don dagaro da kai.

Ya ce wannan tunani ya sa suka ga dacewa su talafa wa gwamnati ta sauke nata nauyi ta bai wa matasa horo don su sami ƙwarewa a kan sana’o’i na hannu.

A wannan karo sun horas da mutune 460 da aka yaye, wasu sun koyi haɗa sola, wasu kwalliyar mata, wasu girki-girke da sauran abubuwa da dama.

Ya ce zuwa yanzu wannan shi ne karo na shida da suke koyawa matasa sana’o’i da yaye su, amma ba wani tallafi na kai tsaye da suka taɓa samu daga gwamnati, amma akwai jagorori da suka gayyata da suke sa ran baivwa waɗanda aka yaye tallafi da za su iya gina sana’o’i da suka koya.

Muhammad Mubarak ya’ce iyayen yara na ba su haɗin kai, wasu ma da kansu suke kawo ‘ya’yansu, kuma suna yabawa da irin hazaƙa da suka ga ‘ya’yansu ke yi na kafa sana’o’i suna taimaka wa iyaye da sauran ‘yan’uwa.

Muhammad Mubarak ya ce a karon farko sun yaye ɗalibai 120 na biyu guda 80 na uku 120 na huɗu 80 na biyar 388 sai wannan karo na shida sun yaye guda 460.

Shi ma BKB Abdalla na Ambassada Yusuf Ogan Biye, wanda ya wakilci Ambasada Alhaji Ibrahim Iliyasu Ogare shugaban kasuwar Idora a Legas, ya bayyana cewa ƙoƙarin Matasan Arewa Family abin a yaba ne sosai. Sun yi ƙoƙari 100 bisa 100, “Domin duk wanda zai tsaya ya koya maka sana’a ka dogara da kanka ka taimaki al’umma abu ne mai kyau”, in ji shi.

Ya shawarci waɗanda ke gudanar da horon su ƙara hoɓɓasa na ƙara jawo yara da koya musu sana’o’i domin suna so a riƙa alfahari da al’ummar Kano da na Arewa a kan tsayawa a kan sana’a na dogaro da kai duk inda suka shiga a ciki da wajen ƙasar nan.

BKB Abdallah ya miƙa saƙon tallafi kuɗi da Alhaji Ibrahim ya turo shi da su ga Matasan Arewa Family. Ya ce shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Hon. Yusuf Ogan Boye zai duba ya yi abin da ya cancanta shi ma kamar yadda dama ya saba aikin alheri a yankin Arewa da ma kudancin ƙasar nan.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History