Matatar Dangote Ta Fara Aiki


Babbar matatar man fetur da ke cibiyar kasuwancin Nijeriya ta fara aiki da sanyin safiyar Juma’a. Hakan ya biyo bayan isar da danyen mai ganga miliyan shida ga matatar.

Duk da cewa ya kamata a fara aiki a watan Yunin 2023, matatar man da hamshakin dan kasuwar nan da ke Kano, Aliko Dangote ya gina ta samu danyen mai na farko a karshen shekarar da ta gabata a wani mataki na fara aikin da aka samu jinkiri.

Matatar dangote mai karfe tace mai ganga 650,000 a kowace rana ana yi mata ganin ita ce mafi girma a nahiyar Afirka, ana ganin za ta iya kawo sauyi ga tattalin arzikin Nijeriya idan ta fara aiki gadan-gadan ta hanyar kawo karshen dogaron da kasar ke yi kan shigo da man fetur daga kasashen ketare.

Aikin farko dai zai kasance na samar da man jiragen sama kafin a ci gaba da fitar da mai, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Duk da cewa Nijeriya na daya daga cikin manyan kasashen da ke hako mai a nahiyar Afirka, kuma mafi karfin tattalin arziki a nahiyar, amma ta dogara ne kacokan kan man fetur da dizal da ake shigo da su daga kasashen waje saboda rashin iya tacewa.

Shigo da mai da tallafin man fetur ya haifar da koma baya ga kudaden waje da Nijeriya ke samu a daidai lokacin da kasar ke fama da raguwar kudaden shigar mai da kuma karancin kudaden kasashen waje.

“Kamfanin matatar mai na Dangote zai iya samar da kashi 100 na abubuwan da Nijeriya ke bukata na dukkan kayayyakin man fetur, dizal, kananzir, da man jiragen sama, sannan kuma za ta iya samun rarar kowanne daga cikin wadannan kayayyakin domin fitar da su zuwa kasashen waje,” in ji kamfanin.

Ginin matar dai ya kai hekta 2,635 (kadada 6,500) na fili a yankin hada-hadar oh kasuwanci na Lekki da ke gefen birnin Legas, kuma kimarsa ya kai Dala biliyan 19.

Matatar man da aka shirya fara budewa a shekarar 2021, shugaba Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da ita a hukumance a shekarar 2023.

Tun bayan hawansa karagar mulki a watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya cire karshen tallafin man fetur da aka dade ana ce-ce-ku-ce a kai, tare da shan alwashin kawo sauye-sauye a fannin tattalin arziki da ya ce zai jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje da kuma samar da ci gaba na dogon lokaci.

Tsohon gwamnan na Legas ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi hakuri da shirin nasa na kawo sauyi, ganin yadda hakan ya haifar da tashin gwauron zabo, da faduwar darajar Naira, da kuma tsadar rayuwa.

Yayin da matatar man Dangote ta fara aiki, ana kuma sa ran matatar mai ta Fatakwal za ta dawo da aiki kamar yadda take yi a baya.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History