Ministan Gidaje Ata Ya Nemi Iyayen Ɗaliban Makarantar Thimarul Ƙur’an Tahafizu Fagge Su Riƙa Biyan Haƙƙoƙin Makarantar Yadda Ya Dace

Daga Ibrahim Muhammad

An yi kira ga iyaye su cigaba da jajicewa su wajen sauke nauyin haƙƙin biyan kuɗin wata wata da na zangon karatu a makarantar Thimarul Qur’an Tahfizul Islamiyyu da Firamare Fagge domin haƙƙi a kansu yake ba a kan gwamnati ko wani ɗan siyasa ko ɗan kasuwa ko ma’aikaci ba.

Shugaban ƙungiyar iyaye da malaman makaranta na makarantar Islamiyya ta Thimarul Qur’an Tahafizu da Islamiyya Firamare.

Ƙaramin Ministan Gidaje na Nijeriya, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ne ya yi kiran a yayin walimar yaye ɗalibai karo na 14 da aka gudanar a harabar makarantar da ke masallacin Juma’a na Abdullahi Bayero da ke Fagge.

Ya ce abin takaici sai iyaye su riƙa bayar da fifiko wajen biyan makuɗan kuɗaɗe dubban Nairori a zangon karatu a makarantun reno na zamani, amma a wannan makarantar a ce su biya abin da bai wuce N1,500 ba a wata ko zangon karatu, amma sai su gaza biya. “Wannan abu akwai damuwa,” in ji shi.

Ya ce ilimi da ake bai wa fifiko na zamani abu ne mai kyau, amma ba daidai bane a riƙa fifita ilimin rayuwar duniya da ba shi kulawa fiye da na addini ba domin wajibi da za a yi wa iyaye hisabi a kan irin ilimi da tarbiyya da suka bai wa ‘ya’yansu. Idan sun kai su makarantar addini shi ne sun ba su kulawa sosai sun a nan za su koyi karatun Ƙur’ani da na addini su san yarda za su bauta wa Ubangiji idan suka kai shi suka tsaya masa ya yi karatun sun tsira, amma bai wa ilimin zamani fifiko domin ya je ya zama Farfesa ko wani Injiniya a ilimin rayuwa ba za a tambaye ka a kai ba, kuma ba su da hujjar fifita kula da ilimin zamani a kan na addini.

Ya yi nuni da cewa ɗan abin da ake biya na kuɗin wata ko na zangon karatu da shi ake tattarawa ake biyan malaman makarantar da duk wata idan iyaye ba su biya wannan kuɗin na makaranta yadda ya kamata ba ana cikin damuwa.

Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya ce, tun a baya can yake yin ta yin kira ga waɗanda suke gudanar da tafiyar da makarantar cewa su samu a ɗora ta a kan gwadabe da za ta cigaba da wanzuwa ko da babu taimako tun yana ɗan Majalisa har ya zama kakakin Majalisar Kano yau, kuma ga shi yana Minista, kuma iyaye ne kawai za su riƙa wannan abu bai kamata a ce haƙƙi a kanka yake ba, kuma ka dogara da wani sai ya zo ya yi maka don yana roƙon iyaye don Allah su cigaba da taimakawa saboda a riƙa biyan malamai ba sai an zo a nce wasu su cika kuɗi sannan za a biyan albashi ba.

Ya gode wa dukkan mutane waɗanda suke a raye da waɗanda suka rasu bisa irin ɗimbin taimako da suka bai wa makarantar. Ya kuma gode wa Hakimin Fagge Sarkin Fadan Kano, Alhaji Ado Kurawa da Dagatai da masu unguwanni da malamai da suka sami halartar taron saukar.

Ƙaramin Ministan Gidajen Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya gode wa iyayen yara da suke ba su amanar ɗalibai suke koyar da su domin shi kansa tun a 1992 yake cikin kwamitin makarantar ya soma daga Sakatare Janar har kuma yau sama da shekaru shida ke nan yana riƙe da shugaban iyaye da malamai na makarantar.

Ya ce wannan ba ƙaramin abu ba ne na jin daɗi a ransa, saboda duk da harkokin siyasa da na mulki da yake ciki ba ya hana shi ya shigo cikin wannan tsarin addini da dama sun shiga tsarin siyasa ne don yin irin wannan hidimar, kuma har yanzu ba su zame a kai ba.

Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya ce su dama maƙasudin siyasarsu shi ne saboda su taimaka wa al’umma da kare addinin Musulunci, kuma ya gode wa Allah da har wannan makarantar ta Thimaru ta kai ga cigaba kafa Sakandare a ciki har sun kai ga yin sauka karo na 14 na ɗalibai 180 wannan alama ce ta Allah ya yi wa makarantar albarka, kullum ana samun karuwar ɗalibai wannan ba ƙaramin alkhairi ba ne.

A yayin taron walimar, mutane da dama sun ba da gudunmawa ga makarantar ciki har da tsohon ɗan takarar Majalisar Tarayya a jam’iyyar PDP na Fagge a zaɓen 2023, Hon. Aƙibu Sani Nabayye da jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Sagir da Ministan Gidaje Yusuf Abdullahi Ata da sauran mutane sun bayar da tallafin kuɗaɗe.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History