Daga Ibrahim Muhammad
Rashin da aka yi na Alhaji Aminu Ɗantata ba na iyalinsa ba ne kawai na al’umma ne, domin mutum ne mai taimakawa da son ganin ‘yan kasuwa sun tsaya da ƙafarsu, yana tallafa musu da jari da koya musu kasuwanci na zamani da taimaka wa matasa.
Manajan daraktan hukumar Kogunan Haɗejia da Jama’are, tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a gidansa da ke Unguwar Ƙoƙi.
Ya ce saboda irin kyakkawan nufinsa kowa ya gani Allah ya cika masa burinsa na son a binne shi a Madina kusa da masoyinsa Annabi (SAW), kuma tafiya ta jana’izasa a Madina ya sa shugabanni a ƙasar nan sun ajiye bambamcin siyasa da rashin jituwa aka je aka yi wa jana’zar.
Alhaaji Rabi’u Sulaiman Bichi ya ce, wannan ya nuna ya kamata ‘yan baya su yi koyi da irin halayensa na rungumar kowa.
Mutane da suka amfana da shi sun sami natsuwa wajen tafi da rayuwa mai albarka, kowa yana yi masa fatan alkhairi da kyakkyawan addu’a.






