Ranar Masu Haɗa Magunguna Ta Duniya A Kano: B-Medix 24 Ta Duba Marasa Lafiya Kyauta


Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana ranar 25 ga watan Satumba da cewa muhimmiyar rana ce ga duk ƙwararrun masu ilimin haraɗa magani a duniya saboda haka masana ke ware abubuwa da yawa don tunawa da irin gudunmawa da masu magunguna ke bayarwa ga kiwon lafiya a duniya.

Pharmacy Ibrahim Mujtaba Janarl Manajan wajen sayar da magunguna na B-Medix 24 ne ya bayyana hakan a lokacin bukin ranar harhaɗa magunguna ta duniya.

Ya ce a kowace shekara rana irin wannan suna shirya abubuwa daban-daban da za su amfanar da masu haɗa magungunan su kansu da sauran al’umma baki ɗaya, kamar a bana sun je asibitin Best Choice, ɗaya daga cikin ɓangarensu suka gabatar da maƙaloli kala-kala. Sun yi magana kan gudunmawar da masu haɗa magunguna za su bayar wajen magance cutar Maleriya da wayar da kai kan sabuwar cutar Maleriya da ta ɓullo yanzu da take haddasa zubar jini da yadda in aka ga alamomimta za a yi ƙoƙarin garzayawa asibiti.

Pharmacy Ibrahim Mujtaba ya ce za su je makarantun Sakandare domin gabatar da jawabi ga ɗalibai domin wayar masu da kai a kan abin da ya shafi illar tamamali da miyagun ƙwayoyi da ba su shawara da nuna musu yadda mai sha’awar hanyoyin da mai son yin karatun haɗa magunguna zai bi don kai wa gaci nan gaba.

Ya ce taken ranar masu haɗa magunguna ta bana shine “Thinks well things Pharmacist”. Ma’ana duk lokacin da kake tunanin lafiya, ka yi tunanin masu haɗa magunguna saboda irin gudunmawar da suke bayarwa.

Ya ƙara da cewa sakamakon wannan rana sun gudanar da duba marasa lafiya kyauta da yi musu ragin kashi biyar ga duk wanda ya sayi magani, kuma tun safe har zuwa ƙarfe 10 na dare duk wanda ya zo za su duba shi kyauta.

Janar Manaja na B-Medix24
ya yi nuni da cewa akwai ƙarancin sanin ƙwararrun masu haɗa magunguna a tsakanin jama’a da gudunmawa da suke bayarwa. “Da can da muke yara, in an ga Pharmacist sai a ɗauka mutum ne kawai da yake zaman chemist. Saboda haka in ka je karatun ma za a ce ka za ka gama ka zo ka yi zaman chemist ne. Wannan ta sa mutane sun raina abin sakamakon hakan,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Harkar magunguna ta fi ƙarfin haka. Abu ne da ake tun daga kan binciken magani zuwa haɗa shi da rarraba shi da sayar da shi, zuwa kawo shi da sayarwa a chemist ɗin. Aiki ne na mai haɗa magunguna, amma wanda mutane suka fi sani kai tsaye, shi ne suke alaƙanta shi da cewa iyakar abin ke nan. Ko in an ga mutum yana ba da maganin a asibiti a yi tunanin cewa in ka zama Pharmacist abin da za ka yi ke nan. Alhali ba haka abin yake ba.”

Mujtaba ya ce sannan kuma akwai ƙarancin makarantun da ake karatun haɗa magunguna, kuma dokoki da ƙa’idodi da aka sa kafin iya samun gurbi a irin makarantun, yana da matuƙar wahala, amma abu mafi muhimmanci idan al’umma ta fahimci matsayin abin da irin gudunmawa da ake bayarwa da damarmaki da ake samu yana da muhimmanci a samu ƙwarewa a fannin.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?