An bayyana rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwa, Dattijo a jihar Kano da ƙasa baki ɗaya, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata da cewa babban rashi ne ba kawai ga al’ummar jihar Kano ko Nijeriya ba, amma ga dukkan yankin Afrika da sauran ƙasashen duniya ne da yake mu’amala da su.
Fitaccen ɗan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ɗanyaro, wanda shi ne shugaban dattawan ‘yan kasuwar Muhammad Abubakar Rimi ta Sabon Gari da Singa ne ya bayyana hakan a saƙon ta’aziyya da nuna alhini da rasuwar ga al’ummar Kano.
Ya yi nuni da cewa al’umma, musamman tun daga kan talakawa, almajirai da malamai na addini da masana na boko sun yi rashin masoyinsu domin kowace kafa ta al’amarin mutane yana shiga.
Ya ce, “Alhaji Aminu Ɗantata yana taimakon addini, yana taimakon harkar kula da lafiyar al’umma, ya taimaka wajen ciyarwa da shayar da mabuƙata da tallafawa harkokin ilimi. Hatta wanda ba a haifa ba ma za su ci gajiyar irin taimako da ayyukan alkhairi da ya yi a rayuwarsa.”
Ya ƙara jaddada addu’ar Allah ya yi wa Alhaji Aminu Dogo rahama, ya kyautata bayansa, ya yi musu albarka, ya sada shi da Annabi Muhammad (saw), ya yafe masa kurakuransa. “Ayyukan da ya yi na alkhari ba za su lissafu ba, ba su da adadi. Allah ya dube shi da su ya yi masa sakayya,” in ji shi.
Ɗanyaro ya ce yana miƙa gaisuwa ga iyalai da al’umma da gwamnati da masarautar Kano da ‘yan kasuwa, waɗanda suka yi babban rashi na mutum mai ƙaunarsu.
Alhaji Ibrahim Ɗanyaro ya ce marigayi Alhaji Aminu Ɗantata shi ne yake shige wa ‘yan kasuwar Kano gaba a kan duk wani al’amari da ya taso ya fi ƙarfinsu, ya warware matsalar ba wanda ya sani.






