Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi da cewa wani bango ne, kuma majingini na addini da kuma masarauta aka rasa.
Tsohon ma’ajin jam’iyyar APC na ƙasa, kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar, Nasarawa tsohon Kwamishina, tsohon ɗan takarar Gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023 a jam’iyyar SDP, Alhaji Bala Muhammad Gwagwarwa ne ya bayyana hakan.
Ya ce daga irin halayya da ya kamata a koya daga Galadiman akwai haƙuri, “Saboda ba za ka taɓa jin maganarsa a kan dukkan wasu al’amura ba, ko kuma ya ɗauki ɓangaranci shi ya sa ma, idan aka lura a lokacin da aka yi jana’izarsa ta haɗa dukkannin ɓangarori na babu wani maganar bambanci.
Ya ƙara da yin nuni da cewa hatta cece-kace da ake yi akan masarautar Kano sai ta sarara saboda kowa na Galadima ne. Saboda haka wani bango ne aka rasa a jihar Kano ta yau,” in ji shi.
Alhaji Bala Muhammad Gwagwarmaya ya roƙi Allah ya maye gurbinsa da makamancinsa, “Irin haƙuri da yake idan duk aka tsaya a kai za a tarar da alkhairi,” ya jaddada.






