Mon. Nov 3rd, 2025

Riƙo Da Al’adunmu Masu Kyau Na Da Muhimmanci Sosai -Hon. Salisu Bebeji

By Saleh Aliyu Oct 26, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana al’adunmu da cewa na da muhimmanci sosai suna ajiye tarihi da ɗabi’u masu kyau da tarbiyya da rayuwa ta addini da usulinmu.

Hon. Dakta Alhassan Salisu Bebeji shugaban ƙaramar hukumar Bebeji ne ya bayyana hakan ya ce rana da gwamnatin jihar Kano ta ware na musamman ta nunin al’adun gargajiya na iyaye da kakanni da aka gada abu ne mai muhimmanci.

Ya ce, “Shi ya sa irin kyawawan al’adunmu, mu cigaba da koyi da su, domin suna tsare yaranmu daga shiga abubuwa na Turawa da abubuwa da ba su kamata ba saboda al’adunmu sun nuna mana yanayi mai kyau.”

Shugaban na ƙaramar hukumar Bebeji ya ƙara da cewa shi ya sa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake ba da dama da kulawa wajen kyautata al’adunmu da addini da kula da tsaro, lafiya da zamantakewa kuma ya bai wa ƙananan hukumomi 44 dama ta kyautata al’adu da zamantakewa.

Ya ce ƙaramar hukumarsa ta Bebeji ta shahara a harkar noma da samar da abinci ba da bunƙasa tattalin arziƙi ana alfahari da ita a jihar Kano ko lokacin Dalar gyaɗa sun ba da gudunmawa saboda ta shahara a noman gyaɗa, masara da sauran kayan abinci.

Dakta Alhassan Salisu Bebeji ya ce suna daga ƙananan hukumomi da suke bunƙasa tattalin arziƙi, saboda noma da kiwo da suke, kuma gwamnatin Kano tana ba su tallafi na taki da kayan noma don inganta noma. “Don haka mun ba da tallafin taki kyauta da maganin fashi da jari ga manoma. Domin haka Bebeji ta zama daga wacce ke bunƙasa tattalin arziƙin jihar Kano da Nijeriya wajen samar da abinci da walwalar al’umma,” ya ƙarƙare.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *