Sanatan Rufa’i Sani Hanga Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Hanya Mai Tsawon Mita 300 A Ƙaramar Hukumar Dala, Kano

Daga Ibrahim Muhammad

Sanatan Kano ta Tsakiya Hon. Rufa’i Sani Hanga ya ƙaddamar da aikin yin wata sabuwar hanya mai tsawon mita 300 a ‘Yan Mata Layin Gasa mazaɓar Gobirawa a yankin ƙaramar hukumar Dala.

A yayin ƙaddamar da aikin Sanata Rufa’i Sani Hanga ya yi kira ga al’ummar yankin a kan su bai wa ma’aikatan da za su yi aikin cikakkiyar goyon baya da haɗin kai a yayin da suke aiki.

Hanga ya ce al’ummar yankin ne suka nemi ya yi musu wannan aikin ya gode wa Allah da ya ba shi dama ya zo don ƙaddamar da aikin yana fatan Allah ya yi masa jagora a kai.

A jawabinsa shugaban ƙaramar hukumar Dala Hon. Suraj Imam ya ja hankalin ɗan kwangila da zai gudanar da aikin ya yi mai inganci, kuma ya san duk aikin da Sanata zai bayar mai ƙwari ne, kuma ba bashi.

A nasa ɓangaren shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Dala, Alhaji Ɗayyabu Ahmad Mai Turare bayyana cewa suna maraba da irin ayyuka da Sanatan na Kano ta Tsakiya yake musu kama daga gina makarantu da tituna da tallafa wa matasa ta horar da su sana’o’i da ba su jari a ɓangarori na sana’o’i daban da shi shaida ne a kai.

Da yake zantawa da ‘yan jarida babban mataimaki na musamman ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Hon. Nura Mai Ƙarfi Dala ya bayyana farin cikinsa bisa wannan muhimmin aiki na titi da Sanata Rufa’i Sani Hanga ya kawo aya mata Layin Gasa a mazaɓar Gobirawa da al’ummar yankin suke da matuƙar buƙatarsa.

Ya ce wannan kawo aikin titin shaida ce a kan jagoransu Sanata Rufa’i Sani Hanga mai sauraren bukatun al’umma ne domin jama’ar yankin su suka je masa da buƙatar a yi titin kuma ya amsa musu ga shi har an zo an ƙaddamar da soma aikin sa.

Hon. Nura Mai Ƙarfi Dala ya ce ba wannan kaɗai ba, al’umma shaida ne a kan irin ɗimbin ayyuka da Sanatan Kano ta Tsakiya yake kawowa a ƙaramar hukumar Dala kama daga gina makarantu da horar da matasa maza da mata a kan sana’o’i da ba su jari da daukar nauyin aikin duba lafiyar al’umma da tallafawa harkar cigaban ilimi a matakai daban-daban da sauran abubuwa da yawa.

Hon. Nura Mai Ƙarfi Dala ya ce irin wannan tagomashi na ayyuka da kulawa da jama’a haka Samata Rufa’i Sani Hanga yake yi a dukkan ƙananan hukumomi da suke ƙarƙashin mazaɓun Kano ta Tsakiya yana kawo ayyuka da za su amfani al’ummar jihar Kano ma gaba ɗaya.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?