Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban Gudanarwa na Hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheik Shehi Shehi Maihula, tare da babban kwamandar Hukumar, Dakta Aminu Ibrahim Daurawa, sun kai ziyarar girmamawa ga mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi II a fadarsa.
Ziyarar na daga cikin bikin cikar Hukumar Hisbah ta jihar Kano shekaru 25 da kafuwa
Da yake jawabi, Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce, sun kai wannan ziyarar ne tare da dukkan shugabannin Hukumar Gudanarwar na Hisbah.
Sheikh Aminu Daurawa, ya ce, yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa domin samar da makaranta da za ta riƙa horar da jami’an Hisbah, domin ƙara ƙarfafa hazaƙarsu kan sha’anin harkokin ayyukansu na samar da tsaro.
A jawabin mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya bayyana gamsuwarsa ga aikace-aikace Hukumar ta Hisbah, musamman a ƙoƙarinta na daƙile ayyukan baɗala a tsakanin al’umma.
Malam Muhammad Sunusi II ya buƙaci Hisbah ta samar da tsari da zai taimaka wajen ƙara wanzuwar haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi, musamman ma malaman addinin Musulunci.






