Sayar Da Kadarorin Gwamnati: Matasan Arewa Sun Bai Wa Atiku da El-Rufai Wa’adin Makonni 2

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar Matasan Arewa da ke da alaƙa da jam’iyyar APC, ta bayyana cewa ƙoƙarin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke yi na yi wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu zagon ƙasa zai ci tura.

Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Mujahid Zaitawa, ya yi zargin cewa abubuwan da Atiku da El-Rufai suka yi a baya, musamman rawar da suka taka wajen sayar da kadarorin ƙasa a zamanin gwamnatin Obasanjo, ya taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙin Nijeriya a halin yanzu.

Zaitawa ya yi tambaya kan inda kuɗaɗen da ake samu daga waɗannan sayar da kadarorin da suka jagoranta suke, musamman irin na su jiragen sama, NEPA, layin dogo, da kuma gidaje na tarayya da sauran abubuwa da dama .

Ya kuma jaddada cewa ‘yan Najeriya ba za su manta da yadda Atiku da El-Rufai suka gudanar da sayar da kadarorinsun da suke neman amsar jin inda aka ajiye kuɗaɗen.

Ƙungiyar ta yi Allah-wadai da yunƙurin Atiku da El-Rufai na komawa kan karagar mulki, inda ta bayyana su a matsayin shugabanni da ba su amfanawa mutane komai ba in ban da sanya su cikin uƙuba.

Zaitawa ya ƙara da cewa ‘yan Nijeriya za su yi watsi da duk wata buƙatarsau ta neman shugabanci, sannan da shigar da ƙara a gaban hukumomin yaƙi da almundahana da cin hanci da rashawa kan zargin karkatar da kuɗaɗen na sayar da kadarorin ƙasa.

Ƙungiyar ta bai wa Atiku da El-Rufa’i wa’adin mako biyu, idan ba su amsa tuhumar da ake musu ba a kan yadda suka sami dama ta tsarin dimakraɗiyya daga yankin Arewa suka jefa ƙasar nan cikin matsalar da yanzu take biyar al’umma ba, za su rubuta wa EFCC da ICPC ƙorafi da zai bankaɗo yadda suke da hannu a kan wannan kadarorin ƙasa da shi ne silar jefa ƙasar nan a mawuyacin hali da ake ciki yanzu.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History