Daga. Ibrahim Muhammad
ADC ta yi zargin cewa wasu na neman haifar da rikici a cikin jam’iyyar bayan amincewa da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi da shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Jam’iyyar ta musanta wasu rahotanni da ake cewa INEC ta amince da shugabanni na jihohi da ta ce yunƙurin haifar da
hargitsi a tsakanin ‘yan jam’iyyar ne.
Jam’iyyar ta ADC ta ce ita ce k eda haƙƙin miƙa sunayen shugabanninta na jihohi, kuma yanzu haka ba ta kammala aikin tattara sunayen shugabannin jihohi ba balle a ce an amince da su.
Faisal Kabir, ɗaya daga masu magana da yawun jamiyyar ta ADC ya ce, waɗannan sunaye ba daga Hukumar Zaɓe suke ba, yanzu abin da suke ƙoƙarin yi shi ne haɗa kan ‘yan jam’iyyar.








