TOPFEED Ta Ƙaddamar Da Sabon Abincin Kaji Masu Ƙwai Ga Dillalan, ‘Yan Kasuwa Da Manoma

Daga Ibrahim Muhammad

Kamfanin Premier Feed Mills masu yin abincin dabbobi na TOPFEED ta gudanar da taro a jihar Kano da dillalan abincin dabbobi da ‘yan kasuwa da masu kiwon kaji, inda ta gabatar musu da sabuwar dusar kaji masu ƙwai ‘Lawyer Wise’ da suka samar.

Mista Choji Fabian manajan kasuwanci mai kula da shiyya Arewa maso Yamma na kamfanin
ya ce, maƙasudin gabatar da abincin kajin masu yin ƙwai shi ne don taimakawa masu kiwon kaji da abinci mai rahusa da auki da za su riƙa samar musu da ƙwai a kan kari, kuma na tsawon shekaru idan an lura da su da kyau.

Ya ce TOPFEED suna yin abincin dabbobi da kaji da kifi sama da shekaru 20. Shi ya sa da suka fito da sabon samfurin abincin kaji na masu yin ƙwai suka gayyaci abokan hulɗarsu da sauran mutane masu kiwo, har ma adadin mutane da suka yi tsammanin za su zo suka zarta yadda suka yi hasashe tun da farko.

Mista Choji Fabian manajan kasuwanci kula da shiyyar Arewa maso Yamma ya ce, suna fata abincin kaji masu ƙwai ya sami karɓuwa saboda sauƙin farashi da aka samu sakamakon kayan abinci da ake sarrafa abincin kaji ya ɗan sauko, don haka suka sauƙaƙa abincin kajin da suke fata masu kiwo za su sami biyan buƙata.

Shi ma shugaban Kamfanin Albarka Poultry Services, Alhaji Yakub Ibrahim, ya bayyana ƙaddamar da sabon abincin kajin da TOPFEED suka yi zai bai wa manoman kaji cigaba, musamman halin da ake ciki na tsadar kaya, samar da sabon samfurin abincin kajin da zai ba da fa’ida.

Ya ƙara da cewa, sun gamsu da yadda kamfanin ke tsare-tsare da ba da kulawa ta yin bincike don samar da abincin kaji mai inganci da sauƙi.

Ya ce kamfaninsu na Albarka Poultry yana samar da aiki ga mutane da yawa. Ana yaye wasu a ƙara ɗaukar wasu.

“Ƙalubalen da muke fuskanta bai wuce na tsadar kaya ba, amma yanzu ana samun sauƙi da cigaba,” in ji shi.

Alhaji Ibrahim Yakub ya yi kira ga manoma su riƙa buɗe tunani, su riƙa samun damarmaki irin waɗannan domin su yi amfani da su. Ya ce in sun sami irin wannan dama za su fi samun riba.

Shi ma manajan gudanarwa na kamfanin Albarka Poultry, kuma mai Kamfanin U.I. Nasiha, Alhaji Umar Ibrahim ya yaba da yadda TOPFEED ke samar da abincin dabbobi. “Ita kaza ba ta fiye jurewa yanayi na canje-canje ba, shi ya sa aka ƙaddamar da wannan abincin kajin a wannan lokaci da ake samun sauyi domin manoma su sami fa’idar abin da take ɗauke da shi,” in ji shi.

Alhaji Umar Ibrahim ya ce su a Albarka sun soma harka noman kaji shekaru 20 da suka wuce, tun suna yin ta da buhu ɗaya, biyu, uku, huɗu, a haka har aka kawo yadda ake ciki yanzu, ana riƙe da ɗimbin ma’aikata, suna kuma da rassa har guda huɗu a wurare daban-daban a Kano.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History