Daga Wakilinmu
Jigo a jam’iyyar PDP, kuma tsohon ɗan takarar Majalisar Tarayya na ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano a 2023, Hon. Ambassador Abdurahman M. Salga, ya nuna matuƙar takaicinsa da rashin kishin al’umma da wasu ‘yan ƙasar nan suke nunawa, musamman ‘yan siyasa daga jihar Kano da a halin yanzu suke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Ambassador Abdurahman M. Salga, wanda shi ne shugaban ƙungiyar PDP Iyali Ɗaya, ya yi nuni da cewa son rai da rashin kishi da tsoro da ƙwadayi suka sa wasu ‘yan siyasa daga jihar Kano ke sauya sheƙa daga jam’iyyarsu suna komawa jam’iyyar APC .
Salga ya yi nuni da cewa jam’iyyar APC a mulkin da take na shugabancin ƙasar nan na baya ƙarƙashin Buhari da na yanzu da ake ciki ƙarƙashin Bola Ahmad Tinubu, babu abin da take sai gallaza wa al’ummar ƙasa da azabtar da su.
“Ta sa su cikin mawuyacin halin da ake ciki, amma wasu ‘yan siyasa suna komawa APC .
Hon Ambassada Abdurahman M. Salga, wanda kuma yana ɗaya daga cikin masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya ja hankali ga matasa maza da mata da sauran al’umma su tashi tsaye kada su kuskura su sake zaɓar duk wani ɗan siyasa da ya koma jam’iyyar APC da a kullum babu abin da take sai gallaza wa al’ummar ƙasar nan tun zuwan ta mulki.






