
A ranar Laraba, 15 ga Mayu, 2024, Abdullahi Usman Tumburkai ya yi nasarar lashe zaben fid da gwani na takarar shugabancin karamar hukumar Dandume a jihar Katsina da ke tafe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman a fannin yada labarai na kwamitin yakin neman zaben, Yusuf Aliyu ya sanya wa hannu, ya tabbatar da cewa an gudanar da zaben ne cikin kwanciyar hankali da lumana.
Abdullahi ya bayyana matukar jin dadinsa game da irin goyon bayan da aka ba shi, inda ya ce: “Ina matukar godiya da kaskantar da kai bisa amincewar da ‘ya’yan jam’iyyarmu suka ba ni. Wannan nasara ta nuna kwazo da sadaukarwar duk wanda ke da ruwa da tsaki a cikin lamarin yakinmu.”
A duk lokacin yakin neman zaben na fid da gwani, Abdullahi ya yi la’akar da muhimman batutuwa da jama’ar yankin ke fuskanta da suka hada da rashin tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da kuma ci gaban aikin gona, inda ya sha alwashin magance wadannan matsalolin da ke damun su idan aka zabe shi.
A matsayin dan takarar jam’iyyar PDP, Abdullahi Usman Tumburkai ya himmatu wajen wakiltar bukatun dukkanin mazabun, tare da yin alkawarin yin aiki tukuru domin ganin an samu sauyi mai ma’ana a karamar hukumar Dandume.
Nasarar da aka samu a zaben fid da gwani cikin lalama, ya nuna goyon bayan da Abdullahi Usman Tumburkai yake da shi a tsakanin jama’a, ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki na jama’iyyar PDP, tare da nuna sha’awar da mutane suka nuna a kan takarar tasa, in ji sanarwar.
Abdullahi, wanda kwararren dan jarida ne, ya nuna karfin gwiwar da yake da ita na lashe babban zaben da ke tafe da za a gudanar da shi a shekara 2025, tare da tsaya tsayin daka a kan kudirinsa na magance matsalar rashin tsaro, inganta ilimi, da kula da harkokin kiwon lafiya domin amfanin dukkan mazauna yankin.
Ya jinjina wa irin goyon baya da karfafa gwiwa da yake samu daga magoya bayan jam’iyyar PDP a yankin da ‘yan mazabarsa, tare da fitattun jama’ar yankin da suka hada da Hon. Abdulaziz Tijjani Dandume, Alhaji Ubale Dandume, Alhaji Danfoloti Dandume, Hon. Hamisu Garkuwa, da shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Alhaji Danlami Dandume.






