Wane Hali Filin Wasa Na Sani Abacha, Kano Ke Ciki?

Daga Ibrahim Muhammad

Tun bayan amincewa da Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta yi a ranar 21 ga Agustan 2024 lna gyare-gyaren filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata, Kani a kan kuɗi N276,734,544 da aka bayyana manufar aikin na yin matsayin gyare-gyare na gaba ɗaya da ya haɗa da shimfiɗar ciyarwa na roba a buɗaɗden babban filin wasan.

Sai dai bayan kammala aikin da sake buɗe filin domin kakar wasannin Ƙwararru na Ƙasa (NPFL) na 2024/25, masu ruwa da tsaki, magoya bayan ƙwallon ƙafa da ’yan wasa sun yi ƙorafe-ƙorafe a kan yadda filin ya kasance na cika da ramuka, tudu, da rashin inganci da ya gaza cimma burin kwangilar.

Zuwa yanzu ba a bayyana sunan kamfanin da aka bai wa aikin ba, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan gaskiya da kuma adalcin da aka yi wajen gudanar da aikin.

Kamar yanda jaridar AHRASJO News ta ruwaito cewa, Kwamishinan Wasanni na Jihar Kano, Hon. Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taɓa bayyana cewa aikin da aka kammala shi ne mataki na farko, kuma aikin ƙarshe na gyaran filin gaba ɗaya zai biyo baya.

Sai dai, yayin da sabuwar kakar gasar wasan ƙwallon ƙafan ta NPFLIKE ke daf da farawa, filin wasan ƙwallon ƙafan na Sani Abacha har yanzu bai kai ga ingantaccen matsayi da ake buƙata ba.

Yanzu dai tambayoyin da ke yawo a tsakanin masoya ƙwallon ƙafa a Kano sun haɗa da mene ne ainihin halin da ake ciki game da filin wasan?Yaushe ne za a fara aikin gyaran na ƙarshe da gwamnati ta yi alƙawari?

Wasu tambayoyi da ke yawo sun haɗa da ta yaya za a tabbatar cewa filin zai cika ƙa’idojin da ake buƙata domin buga wasannin ƙwararru na bana?

A halinda ake ciki yanzu masoya wasanni a Kano na cigaba da jira domin ganin ko gwamnati za ta cika alƙawarin wajen gyara filin wasan cikin gaggawa kafin fara sabuwar kakar wasannin.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History