Wani jami’in ‘Yan sanda a Najeriya dake kula da shiyar Tafa a Jihar Kaduna yaki karbar cin hanci naira miliyan guda daga wani shugaban ‘yan ta’addan da ya kama, wadanda suka hana jama’ar jihohin Kaduna, Neja da kuma Zamfara zaman lafiya.
Kakakin rundunar ‘Yan sanda jihar, Manir Hassan ya ce, DPO’n garin na Tafa ya jagoranci tawagar jami’ansa wajen kama ‘dan ta’addan Bello Muhammad da ya fito daga Zamfara a wani otel dake garin tare da samun sa da kudin da ya kai kusan naira miliyan biyu da rabi da ake zargin kudin fansa ne daga garkuwa da mutane.
Hassan yace yayin bincike, Muhammad ya amsa cewar shi mai garkuwa da mutane ne dake gudanar da ayyukansa a dajin Kagarko dake Jihar Kaduna, kuma kudin dake tare da shi wani kaso ne daga cikin kudin fansar da suka karba.
Jami’in yace a cikin wayarsa an gano hotunansa dauke da bindiga kirar AK47 wanda ‘yan sandan suka kwace, abinda ya sa ya yi tayín bada naira miliyan guda ga DPO’s domin kubutar da kansa, amma baturen ‘yan sandan yaki.
Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kaduna, A. D. Ali ya jinjinawa DPO’n da jami’ansa saboda kokarin da suka yi da kuma kin karbar cin hancin.








