‘Ya Kamata Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Lura Da Gudunmawar Ambasada Yusuf Darma’

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Jama’a da dama musamman a ƙaramar hukumar Birnin Kano da sauran wasu daga ƙananan hukumomin a Kano ta Tsakiya na yaba wa irin gudunmawar da Ambasada Alhaji Yusuf Hassan Darma yake bayarwa a kowane lokaci wajen tallafawa bunƙasa ci gaban al’umma a ɓangarori daban-daban.

Alhaji Yusuf Hassan Darma ɗan kasuwa ne mai tausayi da jin ƙai ganin irin halin ƙuncin rayuwa da al’umma ke ciki.

“Yana tallafa musu a fannoni da dama da suka haɗa da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane, maza da mata musamman masu ƙaramin ƙarfi,” kamar yadda wani ɗan kasuwa Alhaji Abubakar Kanavaro yake tabbatar da hakan bayan wani rabon tallafi da Yusuf Hasan Darma ya yi a Kumbotso.

Alhaji Yusuf Hassan Darma sannanne ne a kan irin gagarumar gudummawa da ya bayar domin tabbatar da samun nasarar Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam a wannan karon ba kaɗai tun daga takararsa na zaɓen 2019.

Ya ƙara da cewa, Alhaji Darma, ya ba da gudunmawa tun daga yaƙin neman zaɓe da lokacin zaɓe har kai wa ga nasara da aka yi a jam’iyyar NNPP da kuma yin tsayin dakan ganin an yi nasara a shari’a har aka tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf.

Wannan ta sa mutane da dama suke kira ga gwamnatin jihar Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam su yi duba da lura da irin gudunmawa da wannan bawan Allah Ambasada Yusuf Hassan Darma yake bayarwa da aljihunsa, “Domin irin su yakamata a jawo su a jiki. Duk abin da za a yi na al’umma a damƙa musu, saboda za su isar da saƙon gwamnati duk inda aka tura,” in ji shi.

Daga irin gudunmawa da Ambasada Alhaji Yusuf Hassan Darma ya bayar har da na sanya fitilu a mazaɓu 13 na ƙaramar hukumar Birnin Kano. Yana kuma raba tallafi ga bunƙasa ci gaban ilimi ta hanyar biya wa yara kuɗin jarabawa da iyaye mata da matasa da jari na sana’o’i.

Malam Aliyu Mamman Maimari, ɗaya ne daga waɗanda ƙungiyar da yake jagoranta ta amfana da tallafin N500,00 daga Ambasada Alhaji Yusuf Hassan Darma ya ce ba shi kaɗai ba, akwai ƙungiyoyi da dama da wasu suka amfana da kuɗaɗe kama daga N250,00 wasu 300,000 har sama da haka, kuma wannan tallafin da ya ba su cikin ikon Allah zai ba su dama na cika burin abin da suka sa a gaba su ma na tallafa wa al’umma a nan gaba.

Jama’a da dama suna kira ga shugabanni musamman gwamnatin jihar Kano da sauran jagorori da yake dama sun san wanene Ambasada Yusuf Hassan Darma da irin gudunmawa da yake bai wa al’umma daga aljihunsa ba tare da yana da wani muƙami a gwamnati ba, a duba a ba shi wani gwaggwabar muƙami da zai daɗa ƙarfafarsa wajen taimakawa ci gaban al’umma.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun